'Yadda Aka Yi Mani Tsirara, Aka Riƙa Lalata da Ni har Na Samu Ciki a Hanyar Libiya'

'Yadda Aka Yi Mani Tsirara, Aka Riƙa Lalata da Ni har Na Samu Ciki a Hanyar Libiya'

Abeokuta - 'Yan Najeriya da dama, musamman mata, kan yanke shawarar tafiya kasashen waje ci-rani, idan talauci da matsin tattalin arziki suka sako su a gaba.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Yayin da wasu kan dace a tafiyarsu, wasu kuma na fadawa komar masu safarar mutane, inda suke fuskantar cin zarafi da duk nau'in bauta, kamar yadda ta faru da Temitope Adenike.

Temitope Adenike ta magantu kan rayuwar da ta yi a kasar Libiya lokacin da ta je ci-rani
Temitope Adenike ta ta ba da labarin rayuwarta a Libiya da yadda aka yi mata ciki a hanya. Hoto: Vangaurd.
Asali: Twitter

A zantawar matashiyar da jaridar Vanguard, Temitope Adenike, ta tuno yadda ta zama karuwar karfi da yaji, har ta samu ciki, tun ma kafin ta isa kasar da za ta je.

Yadda aka ja ra'ayin Temitope zuwa Libiya

Da fari, Temitope Adenike ta ce tana rayuwarta salin alin a matsayin daliba a jami'ar NOU da ke jihar Abeokuta, kafin ta fara sha'awar fita kasar waje neman kudi.

Kara karanta wannan

Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Wata kawar mahaifiyata ce ta cusa mani ra'ayin zuwa Libiya. Ta yi amfani da halin matsin tattalin arziki da nake fuskanta, ta kwadaita mun zuwa aikatau a Libiya.
"A lokacin, buri na shi ne na samu kudin da zan dauki nauyin karatu na. Sai ta ce mun dole na je Libiya na yi aiki na watanni uku, sannan na zama oganniyar kaina.
"Amma tun a lokacin ta fada mun ta Sahara ne za mu je Libiya. Haka na je Shagam, na fadawa mahaifiyata har ta amince, ta sayar da wasu kadarorinta, don na yi tafiyar.
"Ta ce tun da ta Sahara za mu yi tafiyar, dole na sayi jallabiya, gari, da sauran kayayyakin da zan bukata. Ni dai ban taba yin irin wannan tafiyar ba."

- Inji Temitope Adenike.

Yadda Temitope ta shafe wata 4 a hanyar Libiya

Temitope Adenike, ta ce bayan kammala sayayyarta, ta hau mota daga Shagam zuwa Mile 12, sannan daga Mile 12 zuwa jihar Kano, inda suka tsallake iyakar Najeriya.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'an EFCC sun cafke fitacciyar jarumar TikTok, Murja Kunya a Kano

"Daga Kano muka tsallake bodar Najariya, a nan muka rasa hanyar sadarwar wayoyinmu. Muka fara tafiya zuwa Agadez, kasar Nijar. Daga nan ne suka fara asalin tafiya a Sahara.
"Sai da muka shafe watanni uku muna tafiya a Sahara, daga Agadez zuwa Libiya. Akwai wani wuri da muka tsaya, muka hadu da wasu 'yan Najeriya da za su ketare tekun maliya.
"Lokacin da muka shiga garin 'Saba', wani mutumi ya zo ya dauke ni, ya kira ita kawar mahaifiyata ya fada mata na iso. Ba ta waiwaye ni ba sai bayan mako biyu."

'Yadda aka sayar da ni a Libiya' - Temitope

Matashiyar ta bayyana cewa bayana cewa ta bar Najeriya a watan Juli, ta isa Libiya a watan Satumba, wanda ya sa matar ta ce tun da ta dade a hanya, dole tana bukatar kudi.

Temitope ta ci gaba da cewa:

"Matar ta ce tana bukatar kudi, don haka ta sayar da ni ga wani dan Ghana. Kuma wanda ya saye ni, ya saye ni ne a matsayin amaryarsa, kuma zan je in yi masa aiki matsayin mata.

Kara karanta wannan

Wata mata ta rasu a wani irin yanayi yayin tafsirin Kur'ani a Abuja

"Kun san na fada maku, ta ce mun a cikin watanni uku zan zama oganniyar kaina, ashe abin ba haka ba ne, sai da na shafe watanni 18, sannan na samu 'yanci.
"Na yi kuka har na gaji. Wannan tafiya ce da ba komawa, ko na ce zan koma, ta ina zan fara, domin ba abin da na baro a gidan, kuma yanzu ma ba ni da komai, dole na daure."

"An yi lalata dani har na yi ciki" - Temitope

Temitope ta magantu kan cikin shege da aka yi mata a hanyar Libiya
Temitope Adenike: 'Yar Najeriya da ta je Libiya, ta ba da labarin ukubar da ta sha. Hoto: Vangaurd.
Asali: Twitter

Cikin sanyin murya, da tuno rayuwar da ta yi a kasar Libiya, Temitope ta ci gaba da cewa:

"Washe gari, 'yan Ghana suka zo daukata. To na fada maku cewa, an ci zarafi na a kan hanya, an yi lalata da ni har na samu ciki, don haka, dole suka zubar da cikin.
"Sun zubar da cikin don na samu karfin yi masu bauta. Na sha azaba sosai, amma haka na daure. Sun tafi da ni, sun kai ni wuraren da na rika yi masu aiki."

Kara karanta wannan

'Farashin abinci da fetur ya sauka a Najeriya': Minista ya zayyano alheran Tinubu

Matashiyar ta ce ba ta ji da dadi ba a zuwanta Libiya, ba ta taba tsammanin haka rayuwarta za ta koma ba, inda tace sau daya ake bari tana magana da iyayenta a duk wata.

"Na yi da-sani, na gwammace da ma ban yi wannan tafiyar ba. Wasu lokuta, haka zan zauna in yi kuka, har sai na gaji. Amma haka na ci gaba da rayuwa cikin wahala.
"Haka na rika aiki tamkar wata baiwa, kuma abin takaicin, zan ta yin aiki na tsawon wannan wata, har a biya ni kudin, amma wasu za su zo su karbe, ko N5,000 ba za su ba ni ba."

Kalli cikakkiyar hirar a nan kasa:

'Yar Najeriya ta kama aikin noma a Turai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wata ‘yar Najeriya mai digiri, wacce kasuwancinta ke tafiya daidai a ƙasar, ta sayar da komai domin komawa Spain.

Kara karanta wannan

'Yar TikTok ta yi wani irin mutuwa mai ban tausayi, an samu gawarta a dakinta

A sabuwar ƙasar da ta zauna, abubuwa ba su tafi yadda ta zata ba, lamarin da ya sa ta koma aikin noma duk da digirinta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng