Buhari ya amince daliban jami'ar NOUN suyi bautar kasa tare da shiga makarantar lauyanci

Buhari ya amince daliban jami'ar NOUN suyi bautar kasa tare da shiga makarantar lauyanci

- Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin dokar da ta kafa budaddiyar jami'ar Nigeria ta kasa da kasa

- Sake fasalin dokar, zai baiwa daliban jami'ar NOUN yanzu damar zuwa bautar kasa da kuma jami'ar koyon ilimin lauyanci ta Nigeria

- Haka zalika, sa hannu kan dokar ya bada damar samar da wasu cibiyoyi da ake kira cibiyoyin karatu, tare da bada sharudda na samar da wannan cibiyoyin

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sake fasalin dokar da ta kafa budaddiyar jami'ar Nigeria ta kasa da kasa, don baiwa jami'ar damar gudanar da ayyukanta kamar sauran jami'o'in kasar ba tare da wani shamaki ba.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sake fasalin dokar, zai baiwa daliban jami'ar NOUN yanzu damar zuwa bautar kasa da kuma jami'ar koyon ilimin lauyanci ta Nigeria.

Mataimaki na musamman ga shugaban kasar kan fannin harkokin majalisun tarayya (majalisar dattijai), Sanata Ita Enang ya sanar da sa hannun shugaban kasar kan sake fasalin dokar a yayin da yake zantawa da manema labarai a cikin fadar shugaban kasa a Abuja.

KARANTA WANNAN: Kukakn kurciya: Abdulsalami ya ceba zai iya zama shugaban Nigeria yana da shekaru 77 ba

Buhari ya amince daliban jami'ar NOUN suyi bautar kasa tare da shiga makarantar lauyanci

Buhari ya amince daliban jami'ar NOUN suyi bautar kasa tare da shiga makarantar lauyanci
Source: UGC

"Shugaban kasa Buhari ya kuma sa hannu a dokar jami'ar NOUN, wacce zata baiwa jami'ar damar gudanar da harkokinta kamar sauran takwarorinta, wajen samu cikakken iko da kuma gudanar sa ayyuka, musamman wajen kara samar da wasu kwasa kwasai da kuma bunkasa tsarin gudanarwar jami'ar.

"Haka zalika, sa hannu kan dokar ya bada damar samar da wasu cibiyoyi da ake kira cibiyoyin karatu, tare da bada sharudda na samar da wannan cibiyoyin," a cewarsa.

Majalisar wakilan tarayya ta amince da wani kudiri na sake fasalin dokar jami'ar NOU (Cap N6 LFN 19B3 [wanda aka sabunta] ta 2017.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.co

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel