Rashin imani: An kone dan Najeriya 'kurmus' da ransa a kasar Libiya

Rashin imani: An kone dan Najeriya 'kurmus' da ransa a kasar Libiya

- Har yanzu bakar fata fatake na shan wahala da nau'ikan azaba daban-daban a kasar Libya

- Rahotanni sun sha bankado yadda ake cinikin fatake bakar fata a Libya tamkar a lokutan cinikin bayi

- Duk da kungiyoyin kare hakkin bil adama da majalisar dinkin duniya sun sha yin Alla-wadai da abinda ke faruwa, har yanzu ba ta sauya zani ba

An ƙone wani mutum dan ƙasar Najeriya kurmus da ransa a Tripoli, babban birnin ƙasar Libya. Har yanzu ba a kai ga gano ko wanene ba

A jawabin da ta fitar ranar alhamis, gwamnatin Najeriya ta yi tir tare da Allah-wadai da harin da aka kai kan ɗan-ƙasarta.

Rahotanni sun yi nuni da cewa wasu mutum uku ƴan ƙasar Libya ne suka yi wa ɗan Najeriyar kisan gilla a wata masana'anta dake Tripoli.

Wurin yayi maƙwabtaka da Tajoura, inda fatake bakar fata 'yan Afirka ke aiki.

An gano cewa sun watsawa marigayin fetur inda suka cinna masa wuta da ransa.

KARANTA: Wasan sada zumunci: Muhimman 'yan wasan Najeriya 4 sun kamu da cutar korona

Sai dai, har yanzu ba a bayyana dalilin mutanen na aikita laifin ba.

Wasu bayanai sun bayyana cewa wasu baƙin-haure guda uku suma sun ƙone inda akayi gaggawar garzayawa da su asibiti mafi kusa.

Waɗanda ake zargi da wannan ɗanyen aiki matasa ne ƴan shekara talatin kuma tuni suka shiga hannun hukuma.

Rashin imani: An kone dan Najeriya 'kurmus' da ransa a kasar Libiya
Abike Dabiri-Erewa
Asali: Twitter

Shugaban ƙungiyar fatake 'yan Najeriya a ƙasar Libya, Federico Soda, ya tabbatar da afkuwar kisan inda ya bayyana hakan a matsayin hauka da rashin hankali.

KARANTA: NDLEA ta lalata gonar tabar wiwi ta N1.2bn a arewa

Da ta ke maida martani akan lamarin, shugabar hukumar kula da ƴan Najeriya mazauna ƙasar waje (NIDCOM), Abike Dabiri-Erewa, ta yi tir gami da Allah-wadai da ƙona ɗan Najeriyar da mutanen uku su ka yi.

A wani jawabi mai taken 'hari kan Fatake', shugabat ta hukumar NIDCOM ta yi tirr da kashe ɗan Najeriya a Tripoli, Libya.

Jawabin ya samu sa hannun shugaban sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama'a na hukumar NIDCOM, Gabriel Odu.

Hukomomin kare haƙƙin ɗan adam da Majalisar ɗinkin duniya duk sun yi alla-wadai da faruwar lamarin inda su ka bayyana hakan a matsayin hauka da nuna kiyayya a kan bil adama.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayarku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel