Shekaru 100: Tarihi da Muhimman Abubuwa Kan Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi

Shekaru 100: Tarihi da Muhimman Abubuwa Kan Rayuwar Sheikh Dahiru Bauchi

  • A jiya Talata ne babban malamin addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya cika shekaru 100 da haihuwa
  • An haifi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi a ranar 2 ga watan Muharram a shekarar hijira ta 1346 wanda a jiya ne 2 ga watan Muharram 1446
  • Legit ta yi waiwaye kan tarihi da abubuwan da Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya cimma a tsawon shekaru 100 da ya yi a duniya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Bauchi - A jiya Litinin, 2 ga watan Muharram, 1446 a kalandar Musulunci Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya cika shekaru 100 da haihuwa.

Sheikh Ɗahiru Bauchi yana daya daga cikin manyan malaman Musulunci mabiya ɗarikar Tijjaniya a Najeriya.

Kara karanta wannan

1446: Muhimman abubuwa 5 da ya kamata Musulmi Ya Sani Dangane da Shekarar Hijira

Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Bauchi ya cika shekaru 100. Hoto: Sayyid Ibrahim Sheikh Dahiru Usman Bauchi
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa bayanai kan tarihi da wasu abubuwa da babban Shehin ya cimma a rayuwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ina aka haifi Ɗahiru Bauchi?

Bincike ya nuna cewa an haifi Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ne a karamar hukumar Nafada da ke jihar Gombe.

A lokacin da aka haifi Shehin a shekarar hijira ta 1436, karamar hukumar Nafada na karkashin jihar Bauchi.

Ƴaƴa nawa Ɗahiru Bauchi ya haifa?

Rahotanni sun nuna cewa Sheikh Ɗahiru Usman Bauchi ya haifi 'ya'ya kimanin 100 a tsawon rayuwarsa.

Dadin dadawa, a yanzu haka bincike ya nuna cewa yana da jikoki sama da 406 da tattaɓa kunne kimanin 100.

Yaushe Ɗahiru Bauchi ya fara tafsiri?

An ruwaito cewa Sheikh Ɗahiru Bauchi ya fara tafsirin Alkur'ani mai girma tun a shekarar 1948 a jihar Bauchi.

Kara karanta wannan

Tsohon jigon APC ya ba Atiku, Peter Obi lakanin kayar da Tinubu a zaben 2027

Wanda hakan ke nuni da cewa a yanzu haka ya shafe shekaru kimanin 76 yana fassara Alkur'ani a Najeriya.

Al'umma da dama a fadin duniya sun taya Shehin murna ciki har da hadimin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari, Bashir Ahmad kamar yadda ya wallafa a shafin X.

An yi zikiri a fadar Aminu Bayero

A wani rahoton, kun ji cewa gidauniyar Sheikh Dahiru Bauchi ta gudanar da taron zikirin Juma'a a fadar sarki da ke Nassarawa a Kano.

Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da zikirin ne tare da gabatar da addu'o'i na musamman a fadar Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng