Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a Bauchi zai yi tafsirin azumin bana

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a Bauchi zai yi tafsirin azumin bana

- Shugaban darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana cewar a jahar Bauchi zai gudanar tafsirinsa na azumin wannan shekarar

- An dai saba gudanar da tafsirin nasa ne duk shekara a jahar Kaduna

- Ana ganin wannan mataki da malamin ya dauka baya rasa nasaba da barkewar annobar coronavirus wacce ta addabi duniya baki daya

Babban malamin nan na addinin Musulunci kuma Shugaban darikar Tijjaniya a Najeriya, Sheikh Dahiru Bauchi, ya bayyana cewar a jahar Bauchi zai gudanar tafsirinsa na azumin wannan shekarar.

An dai saba gudanar da tafsirin nasa ne a garin Kaduna tsawon shekara da shekaru.

Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a Bauchi zai yi tafsirin azumin bana
Sheikh Dahiru Bauchi ya ce a Bauchi zai yi tafsirin azumin bana
Asali: Facebook

Shehin Malamin ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a yau Laraba, 15 ga watan Afrilu, a garin Bauchi, jaridar Leadership ta ruwaito.

Sai dai ana ganin wannan mataki da malamin ya dauka baya rasa nasaba da barkewar annobar coronavirus wacce ta addabi duniya baki daya.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Buhari ya zaftare kashi 9.1 daga farashin takin zamani don taimaka ma manoma

A wani rahoton, mun ji cewa kwamitin Masallacin Sultan Bello dake garin Kaduna ta yanke shawarar dakatar da gudanar da tafsirin Al-Qur’ani mai girma kamar yadda aka saba yi a cikin Masallacin.

Fitaccen Malamin nan, Sheikh Ahmad Gumi ne yake gudanar da tafsiri a Masallacin a duk lokacin azumin watan Ramadana, amma an samu sauyi a azumin bana saboda COVID-19.

Babban limamin Masallacin, Farfesa Muhammad Sulaiman Adam ne ya bayyana haka, inda yace a bana Malam Ahmad Gumi zai gudanar da tafsirin ne daga wani wuri na daban.

Sulaiman yace Malam Gumi ne kadai zai gudanar da Tafsirin tare da majabakinsa, kuma za’a watsa karatun a kafafen sadarwa na gani da na saurare, da shafukan sadarwar zamani.

Haka zalika, Sheikh Sulaiman ya kara da cewa Masallacin Sultan Bello zai cigaba da zama a garkame har sai lokacin da gwamnati ta bayar da izinin bude Masallatai.

Daga karshe Shehin Malamin ya bayyana dalilin daukan wannan mataki shi ne don dakile yaduwar cutar, don haka ya nemi Musulmai su cigaba da addu’a domin Allah Ya yaye masifar.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel