Matatar Dangote Ta Fara Sayar da Kayan Man Fetur, Farashin Dizal Ya Karye Zuwa N1,225/Ltr

Matatar Dangote Ta Fara Sayar da Kayan Man Fetur, Farashin Dizal Ya Karye Zuwa N1,225/Ltr

  • Matatar man Dangote ta fara sayar da dizal da man jiragen sama ga dillalan mai na Najeriya, lamarin da ya karya farashin dizal din
  • A halin yanzu, ana sayar da litar dizal a kan N1,350 sabanin N1,700 da aka sayar da shi makonnin da suka gabata
  • Mahukunta da kuma dillalai sun bayyana cewa farashin na iya kara yin ƙasa yayin da kuma ake shirin fara dakon fetur a watan Mayu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Legas - Farashin Automative Gas Oil wanda aka fi sani da dizal ya fadi daga N1,700 a kan kowacce lita sabanin N1,350 a Najeriya.

Matatar man Dangote ta fara sayar da dizal ga 'yan kasuwa
Farashin dizal ya koma N1,350/ltr yayin da matatar Dangote ta fara fitar da shi. Hoto: Bloomberg
Asali: UGC

Wannan ragin da aka samu na kusan N350 a cikin 'yan makonni ya faru ne sakamakon fara sayar da dizal din da matatar man Dangote ta yi.

Kara karanta wannan

Shekara 1 a mulki: Jerin ayyukan da Bola Tinubu zai kaddamar a watan Mayu

Dangote na sayar da dizal a kan N1,225

Jaridar The Punch ta ruwaito cewa akalla dizal da ya kai darajar $20bn matatar man ta sayar wa 'yan kasuwar cikin gida a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kowanne dan kasuwa da ya yi rijista da matatar ya samu akalla lita miliyan 1 na dizal daga matatar kai tsaye.

Mahukunta daga matatar man da 'yan kasuwa sun tabbatar da cewa an sayar da dizal din a kan N1,225 zuwa N1,300 kowacce lita, ya danganta da yawan wanda dan kasuwa zai siya.

Wannan na zuwa yayin da matatar ta sanar da cewa za ta fara sayar wa 'yan kasuwar fetur a watan Mayun wannan shekarar.

"Farashin dizal zai fadi kasa" - Maigandi

Jaridar Business Day ta ruwaito Abubakar Maigandi, shugaban dillalan mai na kasa, ya ce fara sayar da mai daga matatar zai karya farashin dizal, fetur, gas da sauran su.

Kara karanta wannan

Sauki ya zo yayin da Dangote ya fara siyar da mai, ya gindaya ka'idoji ga 'yan kasuwa

Maigandi ya ce:

"Farashin dizal zai ci gaba da faduwa saboda matatar mai ta Dangote ta fara sayar da shi. Yanzu haka an fara dakonsa daga Legas."

Wani babban jami'in matatar man Dangote ya shaida cewa matatar ta fara sayar da man dizal, kuma nan ba da jimawa ba za a fara sayar da fetur.

Matatar Dangote ta fara fitar da dizal

Kamar yadda jaridar Premium Times ta ruwaito, babban daraktan kamfanonin Dangote, Devakumar Edwin, ya bayyana cewa an fara fitar da kayayyakin ta ruwa da jirgin sama.

Mr. Edwin ya ce:

"Yanzu haka jirage sun yi layi domin a loda masu dizal da man jirgin sama. Kowanne jirgi na daukar akalla lita miliyan 26, duk da muna kokarin dora masu lita miliyan 37."

A hannu daya, kananun 'yan kasuwa sun bayyana cewa suna kan jiran tantancewa daga matatar domin fara dakon mai.

Kara karanta wannan

Abuja: Mummunar gobara ta tashi a gidan shugaban karamar hukuma

Arzikin Aliko Dangote ya karu

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa attajirin mai kudin Najeriya, Aliko Dangote ya samu ribar sama da dala miliyan 100 a 2024.

Wannan ribar na zuwa ne yayin da kamfanoninsa suka samu karin hada-hada a kasuwar hannun jari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel