Sahun Mutane 2 Rak da Musulunci Ya Halattawa Ciyarwa a Maimakon Yin Azumi
A yayin da ake cikin tsakiyar watan azumin Ramadan na shekarar 1445, Legit Hausa ta tattara bayanai kan mutanen da ciyarwa ta fada a kan su a dalilin shari'a.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Dr. Jabir Sani Maihula ya ce duk wanda ke da lalura ta rashin lafiya kamar misalin ulcer, zai rama azumi ko da kuwa ya yi ciyarwa.
Daga cikin wadanda ciyarwa ta fada a kan su, kamar yadda fitaccen malamin addinin musuluncin ya bayyana, akwai mutum biyu.
Wanene zai yi ciyarwa da Ramadan?
1. Wanda yayi tsufan da ba zai koma matashi ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Wanda likitoci suka ayyana rashin lafiyarsa a matsayin marar warkewa.
Akwai bukatar yin gamsasshen bayani akan wadannan mutane, kamar yadda Dr. Jabir ya nuna, domin mutane da dama na ciyarwa ba bisa doron shari'a ba.
Mata masu juna biyu da shayarwa suna cikin wadanda suke yawan kuskuren nan.
1. Tsufar da ba a komawa matashi
Dr. Jabir Maihula ya ce duk wanda ke da lalura ta rashin lafiya kamar misalin ulcer, zai rama azumi ko da kuwa ya yi ciyarwa, sai idan mutum ya yi tsufan da ba zai koma matashi ba.
A cewarsa, alal misali mutumin da ya haura shekaru 85, zai iya yin ciyarwa, saboda ba zai taba komawa shekarun samartaka da zai bashi damar rama wannan azumi ba.
"Amma matashi dan shekara 40 da ke da lalurar rashin lafiya, ba zai yi ciyarwa ba, saboda yana da karfin jikin da zai iya rama azumi ko da bayan shekaru uku ne."
- Dr. Jabir Maihula
2. Rashin lafiyar da ba a warkewa
Malamin addinin ya kuma bayyana cewa rashin lafiya ba ta sa ayi ciyarwa har sai idan likitoci ne suka tabbatar da cewa rashin lafiyar ba ta warkewa bace.
"Idan mutum yana da ulcer, amma likitoci suka kafa masa sharudda na abubuwan da zai kiyaye domin samun lafiya, to ciyarwa ba ta fada a kansa ba, dole zai rama azumi."
Kuskure ne mutum ya sha azumi saboda ba shi da lafiya alhalin shi ba tsoho tukuf ba ne kuma rashin lafiyarsa ba marar magani ba ce.
Kalli jawabin malamin a nan kasa, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na YouTube:
Mutane 12 da aka ɗaukewa azumi
A wani rahoton kuma, Legit Hausa ta kawo bayani kan wasu mutane 12 da shari'a ta yarje masu su sha azumi a lokacin Ramadan.
Malamin addinin Muslunci, Sheikh Aminu Daurawa, ya ce daga cikin mutanen akwai mata masu jinin al'ada, jinin haihuwa, matafiya, marasa lafiya da sauran su.
Asali: Legit.ng