Daga Malam Daurawa: Mutane 12 da Zasu Iya Shan Azumi a Ramadana
- Watan Azumin Ramadana wata ne mai falala da ake azumtar kwanaki 30 a jere ba ci ba sha da rana
- Azumi na da hukunce-hukunce, ciki har da wadanda suke magana kan ajiye Azumin ko yinsa
- Malamin addinin Islama, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu hukunce-hukuncen yin Azumin
Azumin watan Ramadana na daga cikin ibadun da aka wajabta wa Musulmai, sai dai akwai wasu mutane 12 da aka ba su damar ajiye azumin, ko da yake hukunce-hukuncensu sun bambanta.
A wani bidiyo da BBC Hausa ta wallafa, daya daga cikin malaman addinin Musulunci a Najeriya Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya bayyana wasu mutune 12 da aka yi musu uzurin su ajiye azumi a watan Ramadana.
A cewar sa, wasu daga cikin mutanen za su rama Azumin, wasu kuwa ciyarwa za su yi, yayin da wasu ba za su ciyar ba kuma ba za su yi ramuwa ba.
KU KARANTA: Za Ku Yi Matukar Nadama Idan Aka Sauke Dr Pantami, Gumi Ga ’Yan Najeriya
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wadanda za su rama Azumi:
1. Mace mai jinin al'ada
2. Matar da ta sha Azumi saboda jinin biki
3. Matafiyi
4. Mara lafiya
Wadanda za su ciyar:
5. Mace mai ciki
6. Mace mai shayarwa
7. Mai ciwon kishirwa
8. Mai ciwon 'yunwa
Wadanda ba za su rama ba, kuma ba za su ciyar ba:
9. Yaro
10. Mahaukaci
11. Tsofaffi
12. Mai ciwon farfadiya
KU KARANTA: Osinbajo Ya Bayyana Hasashensa Ga Ci Gaban Najeriya, Ya Ce Za a Samu Zaman Lafiya
A wani labarin, Shugaban Mabiya Shi’a na Kungiyar Harkokin Addinin Musulunci a Najeriya (IMN), Sheikh Ibraheem Zakzaky ya raba kayan abinci na miliyoyin Nairori ga mabukata albarkacin watan Azumin Ramadan, Aminiya ta ruwaito.
Dan sa Muhammad Ibraheem Zakzaky ne ya jagoranci shirin rabon kayan abincin da suka hada da buhunan Shinkafa da Sukari da Masara da Gero a madadin mahaifin nasa.
Awata takarda da ya sanya wa hannu, Muhammad Ibraheem Zakzaky ya ce mahaifin nasa ya bayar da umarnin rabon kayan Azumin ne ga mabukata.
Asali: Legit.ng