Yadda masu ciwon Ulcer za suyi azumin watan Ramadan cikin sauki - Masana

Yadda masu ciwon Ulcer za suyi azumin watan Ramadan cikin sauki - Masana

Wani kwakwaren likitan da ke aiki a Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ilorin (UITH), Farfesa Ismail Adigun ya ce dukkan masu fama da ciwon gyambon ciki (Ulcer) suna iya yin azumi muddin za su kiyaye abincin da ke tayar da ciwon.

A hirar da kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) tayi da Adigun a ranar Asabar a Ilorin, ya ce ya kamata masu ciwon ulcer su lura da ababen abincin da ke tayar musu ta ciwon gyambon ciki.

Ya ce wasu masu ciwon gyambon cikin suna samun matsala ne idan sun ci soyayen abinci yayin da wasu kuma ba su samun wannan matsalar.

Yadda masu gyambon ciki za suyi azumin watan Ramadan cikin sauki - Masana
Yadda masu gyambon ciki za suyi azumin watan Ramadan cikin sauki - Masana
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Su daure mu idan mun yi sata - Gwamnan APC mai barin gado

Likitan ya shawarci masu fama da ciwon su rage cin abinci mai zafi, mai yaji da kuma ababen abinci masu dauke da sinadarin acid da ke iya janyo matsala a cikinsu.

A cewarsa, abinda ya fi dacewa da masu fama da ciwon ulcer da ke son yin azumi shine su rika cin abinci masu dauke da mabanbantan sinadarai da suka hada da abinci masu gina jiki, abinci masu bayar da karfi da kuma ganye.

Ya kuma gargadi masu ulcer su guji abinci masu dauke da acid kamar lemu, lemun zaki, innabi da kuma tumatiri.

"Saboda haka, ya dace masu fama da ulcer suyi takatsantsan wurin cin abinci yayin bude baki kuma ta hanyar cin abinci kadan-kadan.

"Misali, mutum ya fara bude baki da dabino da kuma abinci mara nauyi, daga baya kuma yana iya cin abinci mai nauyi," inji shi.

Watan Ramadana ita ce wata na tara a lissafin kwanakin wata na islama kuma cikin wannan watan ne aka wajabtawa dukkan baligai masu hankali da lafiya yin azumi.

Wadanda aka dauke wa azumi sune wadanda ke fama da ciwo ko kuma matafiya ko wadanda ke cikin wani mawuyacin hali da za su galabaita idan dauki azumi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku latsa: Domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: