Malamin Musulunci Ya Ba Gwamnan CBN Mafita Kan Wa’adin Karbar Tsofaffin Nairori

Malamin Musulunci Ya Ba Gwamnan CBN Mafita Kan Wa’adin Karbar Tsofaffin Nairori

  • Dr. Jabir Sani Maihula ya tofa albarkacin bakinsa a kan halin da aka shiga a dalilin canjin manyan kudi
  • Shehin malamin musuluncin ya roki a kara tsawon wa’adin da aka bada saboda mutane su canza kudinsu
  • Maihula ya ce ko a lokacin da aka bukaci a canza kudin, bankuna su na ta rabawa jama’a tsofaffin takardu

Abuja - Mutane da-dama sun fito su na masu kira ga gwamnatin tarayya da bankin CBN ya tsawaita wa’adin karbar tsofaffin kudi a Najeriya.

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa daga cikin wadanda suka fito su na irin wannan kira har da malamin musuluncin nan, Dr. Jabir Sani Maihula.

Da yake magana a shafinsa na Twitter a ranar Lahai, Sheikh Jabir Sani Maihula ya nuna matakin da bankin CBN ya dauka, zai kawo kunci.

Kara karanta wannan

Da walakin: CBN ya yi sabon batu game da karancin sabbin Naira da aka buga kwanan nan

Masanin hadisin na Manzon Allah (SAW) ya roki hukumomi su duba koken jama’a.

“Wa’adin babban bankin CBN na daina karbar tsofaffin takardun kudi zai jefa mutane a cikin tsaka mai wuya
La’akari da cewa har yanzu bankuna su na raba tsofaffin kudi a lokacin da aka bada.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mu na masu yin kira ga hukumomin da abin da ya shafa, su sake yin nazari a kan wannan wa’adi da aka tsaida.”

- Jabir Sani Maihula

Sababbin kudi
Sababbin kudin da aka buga Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

Wanenen Jabir Sani Maihula

Jabir Sani Maihula ya yi digirin farko a addini ne a jami’ar musulunci ta Madina, sannan ya samu digirgir a shari’a a Landan da PhD a Nottingham.

Mabiya shugaban na gidauniyar Imam Malik Foundation a Twitter sun yi na’am da shawarar da ya kawo, suka gabatar da irin koken da wasu suke yi.

Abin da mutanen Twitter ke fada

Kara karanta wannan

Ndume: Sanatan da Bai Taba Rike Sababbin N200, N500 da N1000 da CBN Ya Buga ba

“Ko a yau ma sai da ATM ya ba ni tsofaffin kudi.”

- Buhari Bawa

Allah ya shiga cikin lamarin Ya Sheikh.

- Faruk Moriki

Maganar gaskiya kenan.

- Sulaiman Danjuma Adamu

Shi kuma wani ya ce babu wadanda yake tausayi irin ‘yanuwansa masu rayuwa a kauyuka.

Wani mai bibiyar malamin a Twitter yake cewa saboda gudun tsoron shagalar da mutane, amma sai ya ce ya san a karshe za a tsawaita wa’adin.

Sanata Ali Ndume bai rike N1000 ba

Ku na da labari Sanata Ali Ndume ya ce idan ba a dauki mataki ba, mafi yawan ‘Yan Najeriya za su shiga kuncin rayuwa kamar yadda ya faru a 1984.

A matsayin Sanata, Ali Ndume yake cewa bai taba rike sabuwar N1000 ba, sau daya kurum ya taba ganin sabon kudin tun a watan Disamba.n 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel