Kotu Ta Tura Mutumin da Aka Kama da Murja Magarkama, Zai Shafe Watanni 6

Kotu Ta Tura Mutumin da Aka Kama da Murja Magarkama, Zai Shafe Watanni 6

  • Kotun Musulunci a Kano ta yankewa Murtala Adamu, matashin da aka kama tare da Murja Kunya daurin watanni shida a magarkama
  • An kama matashin tare da Murja kan laifin haifar da hayaniya da aikata badala a unguwar Hotoro da ke jihar
  • Sai dai kuma an ba shi zabin biyan tara ta N30,000 tare da raba shi da Murja da kuma hana masa shiga unguwar na tsawon shekaru biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Jihar Kano - Wata Kotun shari'ar Musulunci da ke jihar Kano, ta aike wani mutum mai suna Murtala Adamu, gidan gyara hali na watanni shida saboda aikata badala.

Kamar yadda jaridar Aminiya ta ruwaito, an kama Adamu ne tare da shahararriyar 'yar TikTok, Murjanatu Ibrahim Kunya, wacce aka fi sani da Murja Kunya.

Kara karanta wannan

Hukumar Hisbah ta aikawa ‘yan iskan gari sako da aka daure Murja Kunya a kurkuku

Kotu ta daure matashin da aka kama tare da Murja
Kotu Ta Tura Mutumin da Aka Kama da Murja Magarkama, Sai Shafe Watanni 6 Hoto: @yagamen1
Asali: TikTok

Wani laifi matashin ya aikata?

Kotun wacce ke zamanta a unguwar Gama, karamar hukumar Kumbotso ta jihar, ta kuma bai wa matashin zabin biyan tara ta N30,000 kan samunsa da laifin tayar da zaune tsaye da aikata aikin assha.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala, ya sanar da kotun cewa an yi ram da Murtala ne tare da Murja a unguwar Hotoro.

Ya kuma ce an yi kamun ne bayan samamen da dakarun hukumar Hisbah suka kai bayan korafe-korafen da suka samu daga mazauna yankin.

Kotu ta hana matashi shiga unguwar Hotoro na tsawon shekaru 2

Har ila yau, Abidin Murtala ya bayyana cewa laifukan da ake tuhumar Murtala Adamu da aikatawa sun yi karo da sashi na 275 na kundin dokokin final-kot.

Kan haka ne Khadi na Kotun, Mai Shari’a Nura Yusuf Ahmed, ya yanke mai hukuncin daurin watanni shida ko zabin biyan tarar N30,000.

Kara karanta wannan

Hanya 1 tak da jami'an tsaron Najeriya suka dauka don kama 'yan ta'adda cikin sauki

Kotun ta kuma raba huldarsa da Murja ta hanyar shata masu layi a tsakani, wato babu shi babu ita, kuma an haramta masa zuwa unguwar na tsawon shekaru biyu.

Jaridar ta kuma ruwaito cewa Murtala ya rattaba hannu kan takardar kulla yarjejeniyar bayan ya cika ta.

Hisbah ta aike sako ga 'yan iskar gari

A wani labarin, mun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano tayi karin haske a game da matakin da aka dauka a kan Murja Ibrahim Kunya.

Wannan bayani ya fito ne ta bakin Dr. Khadijah Sulaiman wanda tana cikin mataimakan shugaban hukumar Hisbah.

Dr. Khadijah Sulaiman ta zanta da ‘yan jarida a ranar Talata, ta ce lokaci ya yi da za a hukunta Murja Kunya a dalilin aikinta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel