Kunji abun da matan gwamnonin Arewa zasu yi wa matasa da zawarawa?

Kunji abun da matan gwamnonin Arewa zasu yi wa matasa da zawarawa?

Matan gwamnonin arewacin Najeriya 19, sun bullo da wani sabon shiri na musamman wanda zai mayar da hankali wajen wayar da kan matasa akan illar shaye shayen miyagun kwayoyi da kuma tallafawa mata zawarawa, wadanda suka rasa mazajensu.

Kunji abun da matan Gwamnonin Arewa zasu yi wa matasa da zawarawa?
Kunji abun da matan Gwamnonin Arewa zasu yi wa matasa da zawarawa?

Wannan matsala ta shaye shayen miyagun kwayoyi tsakanin matasa ta dade tana ciwa al’umma tuwo a kwarya a duk fadin Njariya, ta dalilin haka ne matan gwamnonin suka bullo da wannan shiri wanda zai fara aiki nan ba da dadewa ba.

Uwar gidan gwamnan jihar Naija, Dr Amina Abukar Sani Bello, ta bayyana cewa matan gwamnonin sun hada hannu ne domin samar da wannan shiri wanda zai samar da dabaru da kuma hanyoyin gano matasan dake shaye shaye, da kuma yadda za a taimakawa wadanda dabi’ar ta shigarwa jiki domin su daina.

KU KARANTA: Sabon rikici ya barke a APC

Da take jawabi a wajan babban taron bayar da tallafin kayan sana’oin hannu da aka ba wasu mata 100, da suka rasa mazajensu a garin kwantagora, Dr Amina ta ce shirin zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Comrade Sa’idu Ibrahim, ne shugaban kungiyar data rabawa matan wadannan kayayyaki ya ce sun kashe kudi sama da Miliyan Biyar wajan sayen kayayyakin da aka rabawa matan domin su ciyar da marayun da aka barmasu cikin sauki. Shugaban ya yiwa matan jawabin cewa kungiyar ta basu kayanne domin su tallafawa marayun da aka barmasu, dan haka ba kayan sayarwa bane.

Kayan sun hada da kekunan dinki da injinan markade da kuma injinan yin taliya, matan sun bayyana jin dadinsu da mika godiya ta musamman akan wannan tallafi da suka samu.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng