“Ka Canja Mani Rayuwa”: Bature Ya Bai Wa Dalibin Najeriya Naira Miliyan 159 Da Sabuwar Mota

“Ka Canja Mani Rayuwa”: Bature Ya Bai Wa Dalibin Najeriya Naira Miliyan 159 Da Sabuwar Mota

  • Wani 'dan Najeriya da ke karatu a waje ya gaza biyan kudin makarantarsa hatta da na hayar gidan da yake zaune a turai
  • Wani bidiyon TikTok mai tsuma rai ya nuna cewa Allah ya kawowa mutumin agaji domin yanzu arzikinsa ta karu da naira miliyan 159
  • Dan Najeroyan mai suna Kayode ya fadi a kasa yana godiya ga baturen kan wannan karamci da ya nuna masa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani 'dan Najeriya ya taki babban sa'a saboda Allah ya tarbawa garinsa nono a lokacin da bai da ko sisi a turai.

Mutumin mai suna Kayode yana a dakin ajiye litattafai yana karatu lokacin da wani mai watsa shirye-shirye a intanet, Zachery Dereniowski ya neme shi.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da makiyaya ne ke jawo wahalhalun da ake sha a Najeriya, inji fasto Ayodele

Matashin ya rasa madafa a turai
An yi wa Kayode kyautar kudi da mota Hoto: TikTok/@mdmotivator.
Asali: UGC

Zuciyar Zachery ta tabu lokacin da ya ji cewa mutumin ya gaza biyan kudin makarantarsa a turai da na gidan da yake haya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amma da farko, Zachery ya roki mutumin ya ba shi abinci, sai mutumin bai bata lokaci ba ya mika masa kwanon abinci.

Cike da jin dadin yunkurin Kayode na bayarwa, Zachery ya mika masa kyautar dala 1000. Sai dai kuma, wannan ne mafarin alkhairan da Kayode ya samu.

Zachery ya dawo da karin kyaututtuka, inda ya ba Kayode kyautar naira miliyan 159, sabuwar mota da nau'urar laftof ta MacBook.

Lamarin ya sa Kayode ya fashe da kukan murna yayin da ya fadi a kasa yana godiya ga Zachery da wadanda suka tattara kudi don inganta rayuwarsa.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan lamarin

@Gidi Studios ya ce:

Kara karanta wannan

Bayan shafe shekaru 5 a turai, matashi ya tattara kudinsa, ya gina dankareren gida a mahaifarsa

"A madadin dukkanin Yarbawan Najeriya, Muna masu godiya gareku ku dukka kan soyayyar da kuka nunawa 'dan uwanmu...Kayode."

@CCbyNiyola |UGC ya ce:

"Kayode!! na tayaka murna sosai. Sunanka ya cika manufarsa a rayuwarka."

@Desola ya ce:

"Wannan ya sa ni kuka. Godiya ga duk wadanda suka sa hakan ya faru ga Kayode, Allah ya albarkace ku dukka, Ubangiji ya aiko masu taimakonku a koda yaushe."

Budurwa ta siya katon gida a turai

A wani labarin, mun ji cewa wata matashiya mai shekaru 22 ta cika da murna yayin da ta zama mai gidan kanta a turai tun tana da kuruciyarta.

Matashiyar (@mkaythecreator) ta cika da farin ciki yayin da ta tsaya a gefen sabuwar motarta kirar Audi da ke fake a gaban gidan. Ta sanya bakar riga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel