Bidiyon Adaidaita Sahu Mai Dauke da Fanka, Talabijin da Kujeru Masu Laushi Ya Burge Kowa

Bidiyon Adaidaita Sahu Mai Dauke da Fanka, Talabijin da Kujeru Masu Laushi Ya Burge Kowa

  • Yanayin yadda wani 'dan Najeriya ya 'kawata keken adaidaita sahunsa ya haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da dandalin soshiyal midiya
  • Wata matashiya da ta shiga adaidaita sahun ta garzaya dandalin soshiyal midiya domin nunawa duniya cikin keken da aka saka fanka, talbiji da sauransu
  • Kyawun adaidaitan ya burge masu amfani da soshiyal midiya da dama, sannan sun jinjinawa mai Keke Napep din saboda fikirarsa

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani bidiyo da ke nuna cikin wani keken adaidaita sahu da aka kawata da ababen more rayuwa ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya.

Keken adaidaita mai kayan alatu
Mai adaidaita sahu ya kawata kekensa da kayan more rayuwa Hoto: @angelblessingchy
Asali: TikTok
"Wato na shiga wani shahararren keken adaidaita a yau, akwai fanka a cikinsa," taken da @angelblessingchy tayi wa bidiyonta da ta wallafa a TikTok.

Kara karanta wannan

Hotuna sun bayyana yayin da babban Malami ya raba kayan abinci kyauta ga mabiyansa

Bidiyon ya nuno cikin hadadden adaidaita sahun. @angelblessingchy wacce ta cika da farin ciki da wata fasinja mace sun ji dadin zama kan lallausan kujerar da mai adaidaita sahun ya saka a ciki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

@angelblessingchy ta shawarci sauran masu adaidaita sahu da su yi koyi da wannan mai adaidaita. Akwai talbijin don kallon fasinjoji, karamin fanka, takardar goge baki da sauran abubuwa da ake samu a gidaje.

Keken ya burge wasu masu amfani da yanar gizo. Hakazalika, wani mutum ya sauya adaidaitarsa ta koma tamfar wata motar alfarma.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani kan adaidaitan da aka 'kawata

M.VICKY :

"Wanne ne adaidaitan Onitsha ko da nice na shiga keken nan wannan talbijin din zai bata."

Mr Bankky ya ce:

"Na taba shiga adaidaitarsa komai sabo ne a ciki, na so shi."

Kara karanta wannan

Kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta nemi a kame dan fafutukar raba Najeriya gida biyu

uchelilian503 :

"Irin wannan adaidaitan zai sa ka mance da inda za ka sauka."

Dubem alonso :

"Ka gwada hawa adaidaitan 'yan wkuzu ka ga aljannar duniya a ciki."

Jenny ta ce:

"Lol wannan dakin mutum ya dauko a cikin adaidaita."

An gwangwaje mai adaidaitan da ya maida kudi

A wani labarin, mun ji cewa Auwalu Salisu matashin nan mai shekara 23 a Kano, wanda ya mayar da maƙudan kuɗi Naira miliyan 15 da wani ɗan ƙasar Chadi ya manta a adaidaita sahunsa a shekarar 2023, ya samu tallafin yin karatu.

Matashin mai adaidaita sahun ya samu tallafin yin karatu har zuwa matakin digiri na uku watau digirin digir, wanda kuɗin za su kai N250m.

Asali: Legit.ng

Online view pixel