Duk da Gwamnati Ta Dauki Mataki, Farashin Gas Din Girki Ya Sake Lulawa Har Ya Haura N1300

Duk da Gwamnati Ta Dauki Mataki, Farashin Gas Din Girki Ya Sake Lulawa Har Ya Haura N1300

  • Farashin iskar gas (LPG) da aka fi sani da gas din girka abinci ya yi wani sabon tashin gwauron zabi a wasu sassa na kasar
  • A halin yanzu, kilo daya na iskar gas din na shirin kai wa N2,000, inda ‘yan Najeriya da su kansu dillalai ke korafin tsadarsa
  • Legit ta zanta da wata mata a Kaduna (Maman Sultan) wadda ta ce yanzu ta koma yin girki da gawayi sakamakon tsadar gas

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Wasu ‘yan Najeriya da dillalan iskar gas a Kaduna da Abuja sun soki tashin farashin iskar gas din tare da yin kira ga gwamnati da ta kawo dauki cikin gaggawa.

Kara karanta wannan

Mutane miliyan 1.25 za su ci gajiyar shirin tallafin Ramadan daga hannun Sanata Yari

Rahoton Legit.ng ya nuna yadda jama'a ke nuna bacin ransu kan yadda tsadar gas din ta zama babbar illa ga rayuwarsu a wannan hali na tsadar rayuwa.

Farashin gas din girki a Najeriya
Farashin gas na neman kai wa N2,000/kg a Najeriya. Hoto: Bloomberg/Creditor
Asali: Getty Images

Gwamnati ta cire harajin VAT a kan LPG

Wannan tashin farashin na zuwa ne duk da cewa gwamnatin Najeriya ta cire harajin VAT daga kudin shigo da gas din domin karya farashinsa da samun sauki ga ‘yan Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ana siyar da iskar gas din girki (LPG) tsakanin N1,300/kg zuwa N2,000/kg a Najeriya, ya danganta da garin da mutum ya ke zama.

NAN ya ruwaito wani dillali mai suna Promise Ajujumbu, shugaban kamfanin Promise of God Gas, yana mai cewa tashin farashin LPG ya faru ne saboda tsadar dala da kudin sufuri.

Tashin farashin gas a duk shekara

Ajujumbu ya bayyana cewa tan 20 na LPG, wanda a baya ake sayar da shi kan Naira miliyan 9, yanzu ya haura zuwa Naira miliyan 19.

Kara karanta wannan

Sanarwar Sarkin Musulmi: An ga wata a wasu jihohin Najeriya, za a fara azumi ranar Litinin

Jaridar Nigerian Tribune ta rawaito cewa dillalan sun bayyana cewa tsadar sufurin na da alhaki wajen tashin farashin gas saboda yawancin kamfanonin sufurin na amfani da dizal wajen dakon kayan.

A cewar rahoton NBS, farashin gas din girki mai nauyin 5kg na karuwa da kaso 12% a duk shekara daga N4.588.75 a watan Janairun 2023 zuwa N5,139.25 a watan Janairun 2024.

Gas ya tashi ga azumi ya zo

Rahoton Legit.ng ya nuna cewa bukatar gas din girki da ake kira Liquefied Petroleum Gas (LPG) ta samu koma baya sakamakon tsadar rayuwa da ake fama da ita.

Maman Sultan Rigasa, wadda ta zanta da Legit Hausa, ta ce ta hakura da amfani da gas a wannan azumin, ta komawa gawayi sakamakon tsadar da gas din ya yi.

"Gas din girki yanzu ya fi karfin talaka, musamman da azumi ya zo, kowa yana kokari ya samu abincin sahur da buda baki, dole ta sa na koma amfani da gawayi a gidana."

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda da makiyaya ne ke jawo wahalhalun da ake sha a Najeriya, inji fasto Ayodele

Gwamnati za ta karya farashin LPG

Tun fa dari, Legit Hausa ta ruwaito cewa, gwamnatin tarayya ta sanar da dakatar da fitar da iskar gas din girki zuwa kasashen waje.

A cewar karamin ministan albarkatun man fetur, Ekperikpe Ekpo, dakatarwar za ta taimaka wajen yawaitar gas din a kasuwannin Najeriya wanda zai karya farashinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel