Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago

Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago

  • Wata matashiyar budurwa yar Najeriya wacce ke rayuwar jin dadi a kasar waje ta dawo gida inda ta zama mai jiran shago
  • Da take wallafa bidiyon sabon aikinta a matsayin mai jiran shagon caca, ta ce tana cikin farin ciki tunda Allah ya barta da ranta
  • Yan Najeriya da dama sun yi martani a wallafar tata yayin da wasu ke al’ajabin abun da ya faru da ita

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

Najeriya – Wata matashiyar budurwa ta je shafin soshiyal midiya don bayyana yadda tayi tawakkali duk da cewar rayuwa ta juya mata baya.

A cikin wani bidiyon TikTok, ta bayyana cewa bayan ta shafe shekaru uku a kasar Larabawa, ta dawo gida ta kama sana’ar bakin hanya, yanzu tana jiran shagon caca ne.

Budurwa
Bayan Shafe Shekaru 3 Tana Aiki A Kasar Waje, Budurwa Ta Dawo Gida Najeriya, Ta Zama Mai Jiran Shago Hoto: TikTok/@khemmite_sugar454
Asali: UGC

Bata yanke kauna ba

A yayin daukar bidiyon, an gano matar tana aiki a na’urar buga caca yayin da take taka rawa. Ta bayyana cewa duk da halin da take ciki, tana godiya ga Allah da ya barta da ranta.

Kara karanta wannan

Bayan Shekaru 3 Da Aure Ba Tare Da Sun Ga Juna Ba, Yar Najeriya Ta Hadu Da Baturen Mijinta A Amurka

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutane da dama sun je sashin sharhi don jinjinawa imaninta. Akwai wasu da suka bayyana cewa sun fuskanci irin haka a rayuwarsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin a kasa:

@Gold.bless ta ce:

“yar’uwa na yi aiki a matsayin mai jiran shagon caca na tsawon shekaru 4 kuma yanzu na mallaki nawa kasuwancin da nake yi, kawai ki zama mai gaskiya sannan ki rage kashe kudi, za ki kai wajen.”

mercy ta ce:

“akwai matsala a wani wurin.”

yourvillagepeople2 ta ce:

“wannan da mamaki faaa. Shekarata ta uku kenan a kasar Larabawa kuma na cimma wasu abubuwa masu kyau.”

oladejodasola ta ce:

“na yi farin ciki saboda kina da rai hakan na nufin akwai babbar rabo a gaba.”

Allah Ya Sauya Labarina: Dan Najeriya Da Ya Taso Cikin Talauci Ya Keta Hazo, Bidiyonsa Ya Yadu

Kara karanta wannan

Zan Siya Gida Kwanan nan A Birnin Lagas: In ji Mai Sana’ar Kifi, Mutane Sun Karfafa Mata Guiwa

A wani labarin, wani dan Najeriya mai suna Ayo Martins ya isa kasar waje duk da cewar ya fito daga gidan talakawa.

Da isarsa filin jirgin sama na Manchester da ke kasar Birtaniya, sai Ayo ya je shafinsa na TikTok don wallafa bidiyon tafiyarsa, yana bayar da cikakken bayani kan yadda rayuwarsa ta sauya. Ya ba mutane da dama karfin gwiwa.

A cikin bidiyon da ya wallafa, Ayo ya ce ba a haife shi a cikin kudi ba, amma Allah ya sauya labarinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel