Jimami Yayin da Fitacciyar Jarumar Fina-finai Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, an Fadi Dalilin Ajalinta

Jimami Yayin da Fitacciyar Jarumar Fina-finai Ta Riga Mu Gidan Gaskiya, an Fadi Dalilin Ajalinta

  • An shiga wani irin yanayi bayan rasuwar fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe a jihar Legas da ke kudancin Najeriya
  • Marigayiyar ta rasu ne a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu a jihar Legas bayan ta sha fama da cutar daji na tsawon lokaci
  • Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Babban Daraktan tace fina-finai, Dakta Shaibu Husseini ya fitar a daren jiya Laraba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Fitacciyar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe ta riga mu gidan gaskiya, kamar yadda TheCable ta tattaro.

Marigayiyar ta rasu ne a jiya Laraba 7 ga watan Faburairu a Legas bayan ta sha fama da cutar daji na tsawon lokaci.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Babban basarake a Najeriya, Joseph Edozien ya rigamu gidan gaskiya

Jarumar fina-finai a Najeriya ta riga mu gidan gaskiya
Marigayiyar ta rasu ne bayan ta sha fama da jinya. Hoto: Ethel Ekpe.
Asali: Facebook

Yaushe marigayiyar ta rasu?

Jarumar kafin rasuwarta a Legas ta fito a fina-finai da dama wanda ta ba da gudunmawa sosai wurin ilmantarwa da fadakarwar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban Daraktan tace fina-finai, Dakta Shaibu Husseini shi ya bayyana haka a daren jiya Laraba 7 ga watan Faburairu, cewar Daily Post.

A cewarsa:

"Na samu labarin rasuwar jarumar fina-finan Nollywood, Ethel Ekpe a yau Laraba 7 ga watan Faburairu."
"Jarumar wacce daga bisani ta dawo Fasto ta mutu ne bayan fama da cutar daji a jihar Legas."

Dan jarida ya riga mu gidan gaskiya

"Tabbas za mu yi rashinta musamman iyalina wanda musamman muka saka sunan 'yar mu a matsayin takwararta, ubangiji ya jikanta."

Har ila yau, a jiya ne masoya harkokin wasanni a Najeriya suka shiga makoki yayin da wani fitaccen dan jaridan wasanni, Kayode Tijani ya rasu.

Kara karanta wannan

Kotu ta garkame malamin addini da matarsa saboda babban laifi 1 da suka aikata

Marigayin ya rasu ne jiya Laraba a asibitin koyarwa na Jami’ar jihar Legas bayan ya sha fama da jinya.

Jarumi Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya

Kun ji cewa fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Jimi Solanke ya riga mu gidan gaskiya a jihar Ogun.

Solanke ya rasu ne a ranar Talata 6 ga watan Faburairu bayan ya sha fama da doguwar jinya.

Marigayin ya rasu ne ya na da shekaru 81 a duniya inda ya ce ga garinku bayan daukarsa zuwa asibiti.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel