Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Fitaccen Jarumin Fim Ya Mutu a Najeriya
- Fitaccen jarumin fina-finan Yarbawa mai suna Sisi Quadri, wanda ya shahara saboda kwaiwayon mata ya riga mu gidan gaskiya
- Kamar yadda rahotanni suka zo wa jaridar Legit, jarumin na Nollywood ya rasu ne sakamakon wani rashin lafiya da ba a bayyana ba
- Hakan na zuwa ne kimanin shekara guda bayan Sisi Quadri ya rasa mahaifiyarsa, lamarin da ya girgiza abokan aikinsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura
Fitaccen jarumin Nollywood, Quadri Oyebanji wanda aka fi sani da Sisi Quadri, saboda kwaikwayon dabi'ar mata a fina-finan Yarbawa, ya mutu.
Rahotanni da ke zuwa ma jaridar Legit ya nuna cewa jarumin, wanda ya mallaki gidan kansa a 2020, ya mutu ne sakamakon wani rashin lafiya da ba'a bayyana ba.

Kara karanta wannan
Bayan shekaru da dama, magidanci ya gano ba shine mahaifin 'diyarsa mai shekaru 18 ba

Asali: Instagram
Tunde Olayusuf ya yi alhinin mutuwar Sisi Quadri
Tunde Olayusuf, wanda abokin aikin marigayi 'dan wasan ne, ya garzaya shafinsa na soshiyal midiya don tabbatar da mutuwar jarumin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake wallafa hoton Sisi Quadri, Tunde ya rubuta:
"Komai na duniyar nan yana bisa yadda Allah ya tsaya, daga Allah muka fito, kuma gare shi za mu koma - Allah ya ji kanka 'dan uwa @iamsisiquadir."
Jaruma Biola Adebayo ma ta yi martani ga mutuwar jarumin yayin da ta rubuta:
"Za a yi kewarka sosai Sisi Quadri Allah ya ji kanka da rahama. Allah ya ba masoyanka gaba daya hakuri."
Ga wallafarta a kasa:
Masu amfani da soshiyal midiya sun yi alhinin rashinsa
lanreadediwura:
"Meeeeee yanzun nan na gan shi a shiri mai dogon zango na Anikulapo da safen nan."
mo_bewa:
"Don Allah."

Kara karanta wannan
Gwamnan Kano ya karya gwiwar Sheikh Daurawa, ya yi murabus daga shugabancin Hisbah
the_may16girl:
"Abun bakin ciki Allah ya ji kansa ya gafarta masa. Karshen zamani Allah ya ba duk na kusa da shi juriyar wannan rashi."
horlarbeesih1:
"Abu mai karya zuciya, bakar Juma'a."
Jarumin Kannywood Cif Aderemi ya mutu
A wani labari makamancin wannan, shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood, Chief Adedeji Aderemi, wanda aka fi sani da Olofa Ina, ya mutu.
Jarumim Nollywood, Saidi Balogun, shi ne ya tabbatar da mutuwar abokin aikinsu a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Alhamis, 4 ga watan Jamairu, 2024.
Asali: Legit.ng