Amfani 7 na man ja ga jikin dan Adam

Amfani 7 na man ja ga jikin dan Adam

Babu shakka bishiyar kwakwar man ja na daya daga cikin bishiyoyi a duniya masu cike da albarkatu. Daga cikin wadannan albarkatun ne akwai mai wanda ke da launin ja.

Ana cire man jar ne daga kwakwar man da bishiyar ke fitarwa. Kwakwar na da launin duhu kuma ana iya ganeta daga kamshinta na daban da kuma dandanonta.

Kamar yadda aka sani, tana da amfani ga lafiya kuma ana amfani da ita a yankunan kudanci da gabas a Najeriya. Tana maganin manyan cutuka masu matukar barazana ga lafiyar dan Adam.

Ana iya amfani da man jan wurin girki don kuwa bata da sinadarin cholesterol. Likitoci na shawartar masu fama da cutukan zuciya da su kiyaye duk wani mai da ke kunshe da cholesterol, hakan yasa suke shawartar a dinga amfani da man ja wurin girki.

Kamar yadda bincike ya nuna na zamani, man ja ta kunshi Fatty Triglycerides kuma ana iya samunta a cikin ababen amfani masu yawa.

Ga 7 daga cikin manyan amfanin man ja ga jikin dan Adam.

1. Ana amfani da ita wurin maganin farfadiya.

A gargajiyance, ana amfani da manja wurin maganin shidewa ga kananan yara. Wannan kuwa yana taka rawar gani wurin yakar cutar farfadiya.

2. Man ja na boye shekaru ga mai amfani da ita.

Sakamakon kunsar Vitamin E da A da tayi, tana kashe wasu alamun tsufa da za su iya nuna wa a jiki.

3. Man ja na sa tsayin gashin kai.

Man ja na bada matukar mamaki a bangaren tsayin gashi. Yana sa cikar gashi tare da hana zubewarsa. Yana kara karfin gashi tare da walkiyarsa.

Amfani 7 na man ja ga jikin dan Adam
Amfani 7 na man ja ga jikin dan Adam. Hoto daga The Pulseng
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Da duminsa: Boko Haram sun yi wa barikin soja 'zobe' a Borno

4. Man ja na taimakawa wurin fitar da miyagun kwayoyin cuta daga jiki.

Ba wai kwayoyin cuta kadai ba, man ja na tsarkake kwayoyin halitta tare da inganta su a jikin dan Adam.

5. Man ja na tausasa fata.

Baya ga boye shekaru da hana tsufa da man ja ke yi, tana tausasa fatar jikin dan Adam inda take cire maikon jikinsa.

Hakan ce ta sa ake amfani da ita wurin yin sabulai da mayuka. Man ja na cire kaikayin jikin kuma.

6. Man ja na daidaita karfin jini.

Sabon bincike ya nuna cewa man ja na inganta yawon jiki a sassan jikin dan Adam. Hakan yasa take daidaita jini tare da kariya daga cutar hawan jini.

7. Man ja na maganin warin jiki.

Sakamakon kamshinta mai karfi, man ja na maganin warin jiki idan ana shafata akai- akai a jiki.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel