Yanzun nan: Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Fitaccen Jarumin Fim Ya Mutu a Najeriya

Yanzun nan: Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Fitaccen Jarumin Fim Ya Mutu a Najeriya

  • Duk wani mai rai zai ɗanɗani mutuwa, fitaccen jarumin masana'antar Nollywood, Cif Adedeji Aderemi, ya riga mu gidan gaskiya
  • Jarumi Saidi Balogun ne ya tabbatar da wannan rashi da Nollywood ta yi ranar Alhamis, 4 ga watan Janairu, 2024
  • Mamacin ya kasannce sananne a fannin sana'ar fim na Yarbawa saboda yadda ya iya karin magana a cikin fina-finan da yake fitowa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finai ta kudancin Najeriya, Nollywood, Chief Adedeji Aderemi, wanda aka fi sani da Olofa Ina, ya mutu.

Jarumim Nollywood, Saidi Balogun, shi ne ya tabbatar da mutuwar abokin aikinsu a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram ranar Alhamis, 4 ga watan Jamairu, 2024.

Kara karanta wannan

Bayan kashe limamin masallacin Juma'a, an sake kashe wani makiyayi a Filato

Marigayi Chief Adedeji Aderemi.
Yanzun nan: Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Fitaccen Jarumin Fim Ya Mutu a Najeriya Hoto: @saidibologun
Asali: Instagram

Balogun ya rubuta a shafinsa cewa, "mu kwana lafiya tauraro Chief Deji Akinremi (Olofa Ina) RIP."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Furodusan fina-finai kuma babban jami’in gudanarwa na Best of Nollywood (BON) shi ma ya tabbatar da rasuwar jarumin.

Aderemi wanda ke riƙe da sarautar Sobaloju na Edeland, ya mutu ne yana da shekaru 73 a duniya.

Wasu abubuwan da ya kamata ku sani

Cif Aderemi sanannen suna ne da ya shahara kowa ya san shi a fannin shirya fina-finan Yarbawa a wannan zamani.

Ya kuma shahara da iya karin magana da karya zance a yaren Yarbawa wanda ke cike makil a cikin fina-finai da wasan kwaikwayo daban-daban waɗanda ya taka rawa.

An haife shi a gidan marigayi Cif AbdulSalam Aderemi da marigayiya Madam Aisha Aderemi ta unguwar Jagun- Olukosi da ke yankin Ede a jihar Osun ranar 15 ga watan Mayu, 2023.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama fasto da wasu mutane biyu kan damfara a Kogi

Ya yi karatun firamare a St. Peters Anglican Primary School tsakanin 1957 zuwa 1962 sannan ya wuce Baptist Secondary Modern School, Ode-Omu daga 1963 zuwa 1965.

Daga baya ya sami horon aikin kafinta da hada-hada a Olukorede Furniture Industry tsakanin 1965 zuwa 1970.

Olofa Ina ya kuma fito a shirye-shiryen talabijin daga cikin su Odetedo, Lakaaye, Kogun Maja, da Ade Oba.

Jerim jaruman Kannywood da suka mutu a 2023

A wani rahoton kun ji cewa Akalla jaruman Kannywood shida ne suka rigamu gidan gaskiya daga watan Janairu zuwa Disambar shekarar 2023.

A yayin da shekarar ke neman karewa, Legit Hausa ta yi waiwaye kan silar mutuwar jaruman da abubuwan da suka faru a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel