Jerin Manyan Kamfanoni 7 Da Suka Amince Za Su Yi Dillancin Mai a Matatar Dangote

Jerin Manyan Kamfanoni 7 Da Suka Amince Za Su Yi Dillancin Mai a Matatar Dangote

  • Yayin da matatar mai ta Dangote ta soma aiki a Najeriya, manyan 'yan kasuwar mai sun yi rijista don fara dillancin man matatar
  • Ya zuwa yanzu dai manyan kamfanoni bakwai ne suka yi wannan rijista, kuma sun kammala duk wata yarjejeniya da matatar
  • Haka zalika, dillalan mai masu zaman kansu a Najeriya su ma za su yi zama a wannan makon don cimma matsaya da matatar mai ta Dangote

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Manyan 'yan kasuwa bakwai a Najeriya sun yi rajista da matatar mai ta Dangote don dillancin man fetur da matatar za ta rinka fitarwa.

Dillalan wadanda ke karkashin kungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya, a ranar Lahadi sun bayyana cewa da zaran sun kammala sa hannu kan yarjejeniyar za su fara dillancin man.

Kara karanta wannan

Dangote ya bayyana wanda ya karfafa masa gwiwar bude matatar mai

Kamfanoni 7 da za su fara dillancin man Dangote
Conoil, Total da wasu kamfanoni 5 da za su yi dillancin man Dangote, cikakken bayani. Hoto: Bloomberg, Aliko Dangote
Asali: UGC

Jerin sunayen kamfanoni 7 da za su yi dillancin man Dangote

Wannnan na zuwa ne bayan da kungiyar dillalan mai masu zaman kansu suka sanar da cewa a makon nan ne za su gama tattaunawa da matatar mai ta Dangote don fara safarar man.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jerin manyan 'yan kasuwa bakwai da za su siyar da man Dangote kamar yadda The Nation ta ruwaito.

  1. 11 Plc.
  2. Conoil Plc.
  3. Ardova Plc.
  4. Mrs Oil Nigeria Plc.
  5. OVH Energy Marketing Limited
  6. Totol Nigeria Plc.
  7. NNPC Retail

Matatar man Dangote ta fara aiki a Najeriya

A ranar Juma'a 12 ga watan Janairu, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa matatar man Dangote ta fara tace mai.

A makon da ya gabata jirgi na biyar dauke da danyen mai samfurin Bonny Light ya sauke kayan a matatar Dangote daga kamfanin mai na masa (NNPC).

Kara karanta wannan

Yusuf vs Gawuna: Sabon hasashe ya nuna wanda zai yi nasara a Kotun Koli a shari'ar Kano

Ana sa ran matatar mai ta Dangote za ta rinka tace danyen mai daga nahiyoyi uku da suka hada da Afrika, Amurka da Asia, wanda kuma ake saka ran zai kawo karshen matsalar mai a Najeriya.

Dangote ya fadi wanda ya karfafa masa guiwar bude matatar mai

Jim kadan bayan fara aikin matatar, attajirin Najeriya Aliko Dangote wanda kuma shi ne shugaban rukunin Dangote ya ce Shugaba Tinubu ne ya karfafa guiwarsa har ya bude matatar mai.

Dangote ya nuna jin dadinsa kan yadda shugaban kasa ya ba shi goyon baya, shawarwari da karfafa masa guiwa tun daga farko har zuwa kammala matatar da fara aikin ta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel