Dangote Ya Bayyana Wanda Ya Karfafa Masa Gwiwar Bude Matatar Mai

Dangote Ya Bayyana Wanda Ya Karfafa Masa Gwiwar Bude Matatar Mai

  • Matatar man Dangote ita ce matatar mai daya tilo mafi girma a duniya, kuma an gina ta ne a jihar Legas
  • Wannan na nuni da babban nasara ga Najeriya karkashin gwamnatin tarayya karkashin jagorancin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Wani abin sha’awa shi ne, hamshakin dan kasuwar ya yabawa Tinubu, NNPCL da sauran su yayin da matatar man ta fara samar da man dizal

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullun

Bayan nasarar da matatar man Dangote ta samu na fara samar da tatacciyar man fetur, shugaban rukunin Dangote, Aliko Dangote ya nuna matukar godiya ga Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu bisa hangen nesa da goyon bayansa.

Dangote ya yi godiya ga Tinubu
Dangote Ya Bayyana Wanda Ya Karfafa Masa Gwiwar Bude Matatar Mai Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, Aliko Dangote
Asali: Facebook

A cewar attajirin dan kasuwar, Tinubu ne ya karfafa masa gwiwar fara aikin matatar man shekaru da suka gabata, rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Kano: Gwamnan Abba ya faɗi gaskiya kan tsoma bakin Shugaba Tinubu a hukuncin kotun ƙoli

Dangote ya yaba ma wadanda suka tabbatar da matatar man

A cewar wata sanarwa da tawagar labaransa suka gabatarwa manema labarai, shahararren dan kasuwar ya tuna irin goyon baya, karfin gwiwa da shawarwari masu kyau da ya samu daga Shugaban kasa Tinubu na ganin an cimma aikin matatar man.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabin sabuwar shekarar 2024, Tinubu ya ce:

"A shekarar 2024, za mu tabbatar mun farfado da matatun man fetur da suka hada da matatar mai ta Fatakwal, sannan matatar mai ta Dangote za ta taimaka wajen cimma hakan."

Musamman, Dangote ya nuna tarin godiyarsa ga manyan masu ruwa da tsaki, ciki harda Shugaban kasa Tinubu da kamfanin man fetur na Najeriya (NNPCL).

Ya gode masu ne kan rawar ganin da suka taka wajen ganin mafarkin matatar ta zama gaskiya, rahoton The Guardian.

Kara karanta wannan

Shehu Sani ya yi shagube ga Betta kan alkawarinta na fitar da yan Najeriya miliyan 50 daga talauci

Ya ce:

“Ina so in gode wa Shugaban kasa Bola Tinubu bisa goyon bayan da ya ba mu da kuma tabbatar da ganin mafarkinmu ya zama gaskiya.
"Wannan aiki, kamar yadda aka shaida a yau, da ba zai yiwu ba in ba don jagorancinsa na hangen nesa ba kuma ya ba da hankali ga bayanai dalla-dalla.
"Sanya baki da ya yi a matakai daban-daban ya kawar da duk wani cikas ta yadda aka cimma aikin cikin lokaci kadan."

Matatar man Dangote ta fara aiki

A baya Legit Hausa ta kawo cewa a ranar Juma'a 12 ga watan Janairu ne aka fara tace mai a matatar man Dangote.

A makon da ya gabata ne aka kawowa matatar jirgin danyen mai karo na biyar samfurin Bonny Light daga Matatar Man Fetur na Kasa, NNPCL.

Asali: Legit.ng

Online view pixel