Hikimomin Dake Tattare Yin Azumi Da Kuma Dalilin Yin Azumi, Dr Jamil Zarewa

Hikimomin Dake Tattare Yin Azumi Da Kuma Dalilin Yin Azumi, Dr Jamil Zarewa

Tsokacin Edita: Mabiya addinin Islama sun fara ibadar azumi cikin watan Ramadana tsawon yan kwanaki yanzu. Tambayoyi sun yawaita kan hikimomi da dalilan da yasa ake wannan azumi.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Dr Jamilu Yusuf Zarewa, Malamin addinin musulunci kuma lakcara a tsangayar nazarin addinin Musulunci dake jami'ar Ahmadu Bello Zaria.

Jamilu
Hikimomin Dake Tattare Yin Azumi Da Kuma Dalilin Yin Azumi, Dr Jamil Zarewa
Asali: Facebook

HIKIMOMIN DA AZUMI YA ƘUNSA

Tambaya:

Assalamu Alaikum. Don Allah Malam a taimaka min da bayani game da dalilin da yasa ake yin Azumi?

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amsa:

Wa alaikum assalam. Azumi ginshiki ne daga cikin turakun Musulunci, waɗanda addinin Musulunci ba zai cika ba sai da su. Allah da Manzonsa sun yi umarni da shi, saboda wasu muhimman manufofi, ga wasu daga ciki:

1. Samun tsoron Allah, saboda mai Azumi yana barin abin da yake so saboda Allah, hakan zai sa ya ƙara samun tsoron Allah.

Kara karanta wannan

Dan Ganduje ya samu muƙami da Tinubu ya dakatar da Shugaban REA a kan N2bn

2. Samun kariya daga Shaiɗan, saboda Azumi yana takure hanyoyin Shaiɗan, wannan yasa zunubai suke ƙaranci a Ramadan.

3. Tuna talakawa da wahalar da suke ciki, saboda duk lokacin da mai kuɗi ya ɗanɗana yunwa zai tuna halin da talakawa suke ciki.

4. Sabawa rai wajen barin abin da take so, da kuma haƙuri akan abin da take sha'awa.

5. Kankare zunubai da kuma samun ɗaukakar daraja, saboda Azumi yana gyara zuciya, da kuma rai.

6. Samun lafiyar Jiki, saboda Azumi yana kariya daga cututtuka masu yawa, kamar yadda likitoci suka tabbatar.

7. Ta hanyar Azumi mutum zai saba da yin aiki don Allah, saboda Azumi sirri ne tsakanin Allah da bawansa.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Asali: Legit.ng

Online view pixel