Ba Zan Aureshi Ba: Budurwa Ta Kori Saurayinta Saboda Ba Ya Shan Taba Ko Barasa
- Dan Najeriya ya wallafa hirarsa da budurwarsa a kafar yada zumunta yadda budurwar ta ce bata son shi a yanzu
- Budurwar ta ce ita fa yanzu bata son shi tunda baya shan barasa ko kuma taba, a cewarta hakan yawa ne
- Ta ce bata son yadda yake rayuwa haka, bai dace mutum ya kasance babu ko daya daga cikin wadannan hali ba
Wani matashi dan Najeriya ya jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter bayan ya wallafa hirarsa da budurwarsa akan rashin shan barasa da kuma taba da yake yi.
@Deevybs ya wallafa hirar tasu ne a kafar sada zumunta ta Twitter inda ya yi rubutu kamar haka “Wasu ‘yan matan basu da tabbas, don kawai bana shan barasa ko taba?”
A hirar tasu, saurayin ya tambayi budurwar tashi cewa me yasa ta ke nuna masa wani irin hali a kwanakin nan, sai ta mayar masa da martani ta ce tana sonshi amma tana da wasu ‘yan matsaloli.
Ta kara da cewa, bata son yanda yake rayuwa babu shan taba ko barasa, Blessing ta ce bai dace ba ace mutum bashi da daya daga cikin irin wannan hali.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mutane da dama sun tofa albarkacin bakinsu akan wannan lamari
@amjustacommoner:
“Me yasa baka shan taba, tana son ta banbance soyayyarka a gareta lokacin maye da sabanin haka, ni ma bazan zama abokinka ba tun da baka shan taba.”
@Dukespri:
“Hhhhh, yarinya ta ki soyayya, ta ce baza ta so mutum kamarsa ba, ka duba madafin ka. Kayi tsafta da yawa, za ki yita korafi akan komai.”
@lemea_jnr:
“Nima na samu irin wannan, a lokacin ne na gane cewa duniya ba yadda nake tsammani take ba.”
@yallmeetbenny:
“In baka shan taba ko barasa, mai sauki ne kai dan yaro ne (mai neman mata).”
"Ni Ba Kowa Bane Idan Ba Ki" Matashi Ya Roki Tsohuwar Budurwarsa Da Sako Mai Sosa Zuciya, Ya Fusata Samari
@Zealkrosszeal:
“Gurbacewar tarbiya ta zamo ba komai ba a wannan duniya tamu.”
@MauriceDBahdGuy:
“Baku san mata basa son mutanen kirki, sun fi son mutanen banza.”
@360hustle01:
“Bana shan taba ko barasa, amma kai na yana yana wuta ba wanda ya isa ya taba ni.”
Budurwar Da Ke Tallan Kanta Da Hotunan Batsa Ta Tuba, Ta Mika Rayuwarta Ga Yesu
A wani labarin, Wata budurwa da ta saba yada hotunanta a kafar sada zumunta don jama’a su gani ta ce yanzu ta sauya rayuwarta, ta dawo cikakkiyar mai bi.
A cewar budurwar, rayuwarta ta sauya tun bayan da ta rungumi tafiyar Annabi Isa a addinin kirista.
Asali: Legit.ng