Jarumai 6 da Suke da Ƙwarewa Ta Musamman a Wasu Fannonin Masana'antar Kannywood

Jarumai 6 da Suke da Ƙwarewa Ta Musamman a Wasu Fannonin Masana'antar Kannywood

Kano - Kannywood na daga cikin manyan masana'antun nishaɗi a Najeriya, inda take taka muhimmiyar rawa wajen wayar da kan al’umma, ilmantarwa da kuma adana al’adun Hausawa ta hanyar fina-finai, waƙoƙi da shirye-shiryen talabijin.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tsawon shekaru, masana’antar ta samar da dubban jarumai, mawaka, daraktoci, furodusoshi da masu ɗaukar hoto, inda kowa ke taka rawar da ya dace da basirarsa.

Fitattun 'yan Kannywood da suka taka rawar jarumai da kuma wasu fannoni a masana'antar
Jaruman 'yan Kannywood, Ali Nuhu (hagu), Adam A. Zango (tsakiya) da Sani Musa Danja (dama). Hoto: @realalinuhu, @adam_a_zango, @realsanidanja/Instagram.
Source: UGC

'Yan Kannywood da suka shahara a wasu fannoni

Duk da cewa mafi yawan ’yan Kannywood su kan zabi fanni daya da suka ƙware a kai, akwai wasu fitattun 'yan wasa suke da kwarewa a fannoni daban-daban na masana’antar, in ji rahoton BBC Hausa.

Wannan mukala za ta waiwayi wasu daga cikin fitattun ’yan Kannywood da suka shahara wajen iya haɗa fannoni fiye da guda, tare da bayyana yadda suka fara, irin gudunmawar da suka bayar, da kuma dalilin da ya sa ake kallonsu a matsayin ginshiƙai a masana’antar Kannywood.

Kara karanta wannan

Ashe harin Amurka ya kashe ƴan ta'adda a Sokoto, wani bidiyo ya ɓulla daga baya

1. Ali Nuhu

Ali Nuhu ya fara ne a matsayin jarumi kafin daga bisani ya dawo ba da umarni da kuma shirya fina finai
Shugaban hukumar fina-finan Najeriya, kuma jarumin Kannywood, Ali Nuhu a cikin falo. Hoto: Ali Nuhu
Source: Facebook

Ali Nuhu Muhammad na daga cikin sunayen da ba za a iya ambaton Kannywood ba tare da tunawa da shi ba. An dade ana masa laƙabi da “Sarkin Kannywood”, ba wai don suna kawai ba, sai don irin rawar gani da ya taka a fannoni da dama na masana’antar.

Ali Nuhu ya fara fitowa ne a matsayin jarumi tun a farkon kafuwar Kannywood, inda ya fito a cikin manyan fina-finai na tarihi da soyayya da suka shahara a wancan lokaci.

Fina-finai irin su Sangaya, Mujadala, Fil’Azal da Gambiza sun taimaka wajen gina sunansa da kuma jawo masa karɓuwa daga masu kallo.

Bayan shekaru yana taka rawa a matsayin jarumi, Ali Nuhu bai tsaya nan ba. Ya shiga fagen bayar da umarni, inda ya nuna yana da basirar jagorantar aikin fim gaba ɗaya.

Daga cikin fina-finan da ya bayar da umarni akwai Sai Wata Rana, Dijangala, Gambiza, da sauransu, in ji wani rahoto na Leadership Hausa.

Kara karanta wannan

Borno: Boko Haram ta saki bidiyon tsohon Mataimakin Ciyaman da ta sace

A zamanin fina-finai masu dogon zango, Ali Nuhu ya ƙara nuna ƙwarewarsa ta hanyar jagorantar manyan shirye-shirye kamar Gidan Sarauta da Alaƙa, wanda suka samu karɓuwa sosai a tsakanin masu kallo.

Haka kuma, mukaminsa a matsayin shugaban hukumar fina-finai ta Najeriya ya kara tabbatar da irin tasirin da yake da shi a masana’antar.

2. Yakubu Mohammed

Yakubu Mohammed ya kasance mawaki kuma fitaccen jarumi a Kannywood.
Yakubu Mohammed, fitaccen jarumi kuma mawaki a Kannywood. Hoto: Yakubu Moahmmed
Source: Facebook

Yakubu Mohammed yana daga cikin ’yan Kannywood da suka fara ne daga wata hanya ta daban, amma suka ƙare da zama tauraro a fannoni daban-daban.

Tun farko, Yakubu ya shahara ne a matsayin mawaki, inda ya yi suna a farkon shekarun 2000 da waƙoƙi masu armashi da suka ɗauki hankalin masoya fina-finan Hausa.

Daga baya, Yakubu ya koma fagen ba da umarni, inda ya bayar da umarni ga fina-finai da dama da suka yi tashe, ciki har da Adamsy, Hawayena, Haƙƙin Miji da Ƙawayen Amarya.

Bayan nasarar da ya samu a ba da umarni, Yakubu Mohammed ya sake komawa gaban kyamara a matsayin jarumi a Kannywood da fina-finan Kudu.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka kutsa har fadar sarki suka sace mutane

A yau, yana daga cikin jaruman da ke jan ragamar fina-finai masu dogon zango kamar Allura Cikin Ruwa, Gidan Sarauta da Garwashi.

Wannan haɗin basira ya sanya Yakubu ya zama ɗaya daga cikin jaruman da ke da cikakkiyar fahimta game da aikin film daga tushe zuwa ƙarshe.

3. Sani Danja

Sani Danja ya shahara a Kannywood a fannin waka da kuma fitowa matsayin jarumi.
Jarumi Sani Danja tare da Yakubu Mohammed a wajen daukar wata talla. Hoto: Sani Danja
Source: UGC

Sani Danja na daga cikin fitattun ’yan Kannywood da suka yi suna ta hanyoyi da dama, cewar wani rahoto na Northern Wiki.

Tun farko, ya fara ne a matsayin jarumi, inda ya fito a cikin fina-finan da suka shahara a lokuta daban-daban, kamar Dan Zaki, Tutar So, Daham da dai sauransu.

Bayan ya daɗe yana fitowa a matsayin jarumi, Sani Danja ya shiga harkar waƙa, inda ya nuna cewa yana da murya da salo da ke jan hankali. Waƙoƙinsa sun zamo abin sauraro a tsakanin masoya Kannywood, kuma da dama daga cikinsu sun shahara a fadin Arewa.

Baya ga zama jarumi da mawaƙi, Sani Danja ya kuma shiga fagen shirya fina-finai a matsayin furodusa. Wannan ya ba shi damar sarrafa ayyukan da yake so, tare da taimakawa wajen samar da fina-finai masu inganci kamar Gidan Danja, Allura Cikin Ruwa da sauransu.

Kara karanta wannan

Hadimin Abba ya fadi abin da ke shirin kora 'yan Kwankwasiyya zuwa jam'iyyar APC

4. Adam A. Zango

Shi ma dai Adam A Zango ya shigo masana'antar ne matsayin mai kida da wake, kafin ya zama jarumi kuma furodusa.
Adam A Zango, fitaccen jarumin Kannywood zaune a kan kujera. Hoto: Adam A. Zango
Source: Facebook

Adamu Abdullahi Zango, wanda ake yi wa laƙabi da Adamu Usher, yana daga cikin jaruman da ke da tarin baiwa a Kannywood. Ya fara ne a matsayin makidin wakoki da kuma rera waka, sannan ya shiga Kannywood gadan gadan matsayin jarumi.

A bangaren wakoki da kuma takara rawa a fim matsayin jarumi, Adam Zango ya jawo hankalin jama’a da waƙoƙi masu armashi da salo na musamman. Waƙoƙinsa sun kasance cikin mafi shahara a masana’antar a lokutan baya.

Har ila yau, Adam Zango ya kasance daga cikin masu shirya fina-finai, inda ya samar da ayyuka da fina-finai da suka taimaka wajen bunƙasa Kannywood kamar Gwaska, Basaja da dai sauransu.

5. Rahama Sadau

Rahama Sadau ta shirya wasu fina finai nata na kanta
Tsohuwar jarumar Kannywood, Rahama Sadau a shigar da ta yi lokacin aurenta a 2025. Hoto: Rahama Sadau
Source: Instagram

Rahma Sadau ta zama ɗaya daga cikin fitattun mata a masana’antar Kannywood, inda ta yi fice ba kawai a fannin jarumta ba, har ma a sauran fannoni.

Rahama ta fara ne a matsayin jaruma, inda ta fito a cikin fina-finai da dama da suka shahara kamar Nadiya, Almajiri, Ba Tabbas da sauransu.

Kara karanta wannan

Yadda gobara ta tashi a kasuwar Sakkwato, ta shafe shaguna sama da 40

Abin da ya bambanta Rahma Sadau da wasu shi ne yadda ta samu damar shiga fina-finan kudancin Najeriya da ma na ƙasashen waje, lamarin da ya buɗe mata ƙofa zuwa duniya.

Baya ga fitowa a fina-finai, Rahma ta shiga fagen shirya fina-finai, inda ta samar da fina finai da suka samu karɓuwa kamar Rariya da sauransu.

A zantawar Legit Hausa da Yusuf Lazio, daya daga cikin jarumai masu kusanci da Rahama Sadau, ya ce:

"Ba za ka san wacece Rahama ba sai ka zauna tare da ita. Tana da saukin kai, ta na da sakin fuska tare da ba kowa dama. Ko yanzu da ta yi aure, ba ta fasa kawo abubuwan da wadanda ke tare da ita za su amfana ba.
"Akwai ayyukan da dama da take shirin yi, kuma idan aka fitar da su, za a kara yarda cewa Rahama ta na da duk abin da ake bukata na samar da fim din da ya dace da zamani."

Yusuf Lazio ya ce Rahama na nan daram a Kannywood, sai dai yanzu ba jaruma ba ce, za dai ta ci gaba da shirya fina-finai, domin ta mayar da abun sana'a kuma wani abu na fikira.

Kara karanta wannan

Matakin da gwamnati ta ɗauka bayan ƴan ta'adda sun kashe fiye da mutum 30 a Neja

6. Hannatu Bashir

Jaruma Hannatu Bashir na daga cikin jaruman Kannywood mata da suka nuna cewa mace ma na iya haɗa rawuna fiye da guda a masana’antar.

Ta fara ne a matsayin jaruma, inda ta fito a fina-finai masu yawa da suka hada da Kotun Ibro, Sarauniya, Shahida, Mutum da Aljan, Kukan Kurciya da sauransu, in ji rahoton Blueprint.

Daga baya, ta koma fagen shirya fina-finai a matsayin furodusa, inda ta jagoranci samar da ayyuka masu ma’ana da suka ja hankalin masu kallo kamar Shaheeda, Ashe Za mu ga Juna da sauransu.

Jaruman Kannywood da suka rasu a 2025

A wani labari, mun ruwaito cewa, masana'antar Kannywood ta yi rashin jarumai biyar a 2025, wadanda da yawansu sun rasu ne suna tsaka da taka rawa a wasu ayyuka.

Daga cikin jaruman Kannywood da aka rasa a 2025 akwai Maijidda Muhammad, wadda aka fi sani da Fulani a shirin fim mai dogon zango na Labarina, a ranar Alhamis, 25 ga Disambar 2025.

Kafin rasuwar Maijidda, Kannywood ta fara girgiza ne da rasuwar Mato Yakubu, wanda aka fi sani da Malam Nata'ala Mai Sittin Goma, wanda ya koma ga mahaliccinsa a Nuwamba, 2025.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com