Zargin Cin Mutunci: Ali Nuhu ya Maka Jaruma Hannatu Bashir a Gaban Kotu

Zargin Cin Mutunci: Ali Nuhu ya Maka Jaruma Hannatu Bashir a Gaban Kotu

  • Fitaccen jarumin Kannywood, Ali Nuhu, ya maka jaruma kuma furodusa Hannatu Bashir a gaban kotu kan zarginta da cin mutuncinsa
  • Tun farko dai zaki Ali Nuhu zai je yin wani fim din Hannatu Bashir ne amma yayi tafiya har aka dage daukar fim din sau biyu
  • Furodusar ta fusata kuma ta tura masa tes mai zafi wanda jarumin ya a alwashin daukar matakin shari’a amma tace masa yayi din

Kano - Fitaccen jarumin masana’antar fim don Hausa, Ali Nuhu, ya maka jaruma kuma furodusa Hannatu Bashir a gaban kotu kan zarginta da ci masa mutunci ta maganganun sakon kar ta kwana da ta tura masa.

Salima Muhammad Sabo wacce ita ce lauyar Ali Nuhu dake ofishin M.L Ibrahim and Co. ta mika karar a gaban kotun majistare dake da lamba 58 a unguwar Nomansland, Kano.

Kara karanta wannan

Dubu ta cika: An kama wasu 'yan Kamaru da kokon kan mutum a Arewacin Najeriya

Ali Nuhu da Hannatu
Zargin Cin Mutunci: Ali Nuhu ya Maka Jaruma Hannatu Bashir a Gaban Kotu. Hoto daga fimmagazine.com
Asali: UGC

Mujallar fim ta rahoto cewa jarumi Ali Nuhu ya kai kara ne saboda hargitsin da suka samu a wani aikin fim don Hannatu wanda bai samu damar zuwa ba duk da yayi alkawari.

A ranar da aka yi da shi cewa zai je yin fim din ta kama 10 ga watan Oktoban 2022 amma sai aka samu akasi yayi tafiya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Saboda rashin zuwansa yasa aka dage daukar bangarensa zuwa rana ta gaba amma duk da haka bai samu zuwa ba, yace a ranar zai dawo kuma ba zai iya samun halartar wurin ba.

Hannah Bashir
Zargin Cin Mutunci: Ali Nuhu ya Maka Jaruma Hannatu Bashir a Gaban Kotu. Hoto daga @insidearewa
Asali: Instagram

Wannan akasin da aka samu ya matukar bata ran Hannatu Bashir wacce ta tura masa sakon kar ta kwana kan cewa bata bukatar aikinsa.

Bayan shigar sakon, jarumin yayi martani mai zafi inda ya zargeta da yi masa rashin kunya. Daga bisani ya sanar mata cewa zai dauka matakin shari’a amma sai tace tana jira.

Kara karanta wannan

Zan Tabbatarwa 'Yan Najeriya Tsaro Kafin Na Mika Mulki, Buhari Ya jaddada

Hannatu Bashir
Zargin Cin Mutunci: Ali Nuhu ya Maka Jaruma Hannatu Bashir a Gaban Kotu. Hoto daga @insidearewa
Asali: Twitter

A karar da jarumin ya shigar, yace shi bai yi wata yarjejeniya a rubuce da Hannatu ba kuma bashi da wata huldar kasuwanci da ita wanda zai sa ta tura masa sako mai dauke da bakaken maganganu domin yunkurin zubar masa da kima da mutunci.

A saboda hakan yake son kotu ta daukar masa matakin shari’a a kanta don bata masa suna da tayi.

Ya hada da hoton sakon da ta tura masa inda ya makala tare da takardar karar da ya shigar gaban kotu.

Ali Nuhu
Zargin Cin Mutunci: Ali Nuhu ya Maka Jaruma Hannatu Bashir a Gaban Kotu. Hoto daga @insidearewa
Asali: Instagram

Tuni kotu ta aikewa jarumar kuma furodusar sammaci mai kwanan wata 11 ga Oktoban 2022 kuma ana bukatar ta gurfana a ranar 18 ga Oktoba domin kare kanta.

Jarumi Ali Nuhu Ya Bayyana Hotunan Matashin Ɗansa Dake Kwallo a Ingila, Ya Birge Jama'a

A wani labari na daban, Sanannen jarumin masana'antar fina-finan Hausa ta Kannywood, Ali Nuhu, ya bayyana hotunan zabgegen saurayin 'dan shi, Ahmad, wanda ke wasan kwallon kafa a Ingila.

Mahaifin mai cike da alfahari da 'dan shi, yayi masa fatan alheri yayin da ya wallafa hoton matashin yana sanar da cewa yana shirin fita wasa ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel