Dandalin Kannywood: Ali Nuhu zai sake shirya Fim din Mujadala don tunawa da Ahmad S Nuhu

Dandalin Kannywood: Ali Nuhu zai sake shirya Fim din Mujadala don tunawa da Ahmad S Nuhu

Zuwa yanzu a iya cewa shirye shirye sun nisa matuka game da sabunta shirin shahararren Fim din nan da yayi suna a shekarun baya, watau Mujadala, sai dai abinda ya ja hankali yan kallo shi ne wanda zai maye gurbin marigayi Ahmad S nuhu.

BBC Hausa ta ruwaito Kamfanin shirya Fina finai na Mai Shadda ne zai dauki nauyin shirya wannan Fim, inda tace a ranar 10 ga watan Mayu ne zata fara nadirsa, haka zalika kamfanin ta bayyana cewar jarumi Umar M Shareef ne zai maye gurbin Ahmad.

KU KARANTA: Gaggan barayin mutane tare da yan fashi da makami su 6 sun fada tarkon Yansanda a jihar Katsina

Shi dai wannan Fim ya shahara a tsakanin yan kallo da masu bibiyan fina finan Kannywood, wanda ya kunshi taurari kamarsu Ali Nuhu, Sani mai Iska, Fati Muhammad, Abida Muhammad, Maijidda Abdulkadir da kuma Ahmad S Nuhu, wanda shine ya fitaccen jarumi a Fim din.

Dandalin Kannywood: Ali Nuhu zai sake shirya Fim din Mujadala don tunawa da Ahmad S Nuhu
Ahmad S Nuhu

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Ahmad ya rasu ne a shekarar 2007 sakamakon hadari da ya rutsa da shi a kan hanyarsa ta zuwa Maiduguri bayan fitowarsa daga garin Azare na jihar Bauchi inda ya gudanar da wasan Sallah.

A zamaninsa, Ahmad ya kasance jarumi mai tashe, domin kuwa tararuwarsa na haskawa, kuma yana da farin jinni a wajen yan kallo, gas hi mutum mai dadin hulda kamar yadda abokansa da na kusa suka tabbatar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel