Dandalin Kannywood: Jaruman fim din Hausa 5 da suka shiga duniyar fina-finan kudu

Dandalin Kannywood: Jaruman fim din Hausa 5 da suka shiga duniyar fina-finan kudu

Yayin da duniyar shirya fina-finai a duniya ke dada dunkulewa wuri daya, a Najeriya ma muna samun irin wannan cigaban inda akan samu jarumai daga wani sashe na masana'antar sukan shiga cikin wani sashe.

A wannan 'yar makalar za mu kawo maku wasu fitattun jaruman fim din Hausa na masana'antar Kannywood 5 da suka shiga duniyar fina-finan kudu.

Dandalin Kannywood: Jaruman fim din Hausa 5 da suka shiga duniyar fina-finan kudu
Dandalin Kannywood: Jaruman fim din Hausa 5 da suka shiga duniyar fina-finan kudu

1. Ali Nuhu

Ko shakka babu Ali ba boyayye bane a masana'antar ta shirya fina-finan Hausa kuma tun da dadewa ma yana cikin wadan da suka fara yin shuhura a fina-finan kudu din.

Wasu daga cikin fina-finan kudun da jarumin ya yin sun hada da Banana Island Ghost da kuma Ojukokoro.

2. Rahma Sadau

Hakika ita ma wannan jarumar ta yi zarra a cikin dan kankanin lokacin da ta soma fitowa a akwatunan talabijin.

Tauraruwar ta haka zalika ta haska sosai a masana'antar fim din kudun bayan da ta shiga wata rigima da kungiyar shirya fim din hausa wanda daga bisani aka kore ta.

Kawo yanzu dai ta fito a fina-finan kudun da dama.

3. Yakubu mohammed:

Shi ma dai wannan ba boyayyen jarumi ba ne a duka masana'antun na gida Hausa da kuma na kudancin kasar nan.

Jarumin dai ya samu wannan damar ta sa ne sakamakon ilimin bokon da ke gare shi tamkar dai sauran jaruman.

Dandalin Kannywood: Jaruman fim din Hausa 5 da suka shiga duniyar fina-finan kudu
Dandalin Kannywood: Jaruman fim din Hausa 5 da suka shiga duniyar fina-finan kudu

4. Maryam Booth

Duk da kasancewar ta mai kananan shekaru, tauraruwar Maryam Booth ta haskaka a dukkan masana'antun biyu inda kawo yanzu ta fito a cikin fina-finai da dama kamar dai sauran jaruman da aka lissafo a sama.

5. Sani Danja:

Kasantuwar jarumin na daya daga cikin wadanda suka assassan sana'ar ta shirya fina-finai a arewacin Najeriya tun shekaru da dama da suka gabata, yanzu kuma jarumin ya lula ya zuwa kudancin kasar inda kuma a can ma ya nuna bajintar sa sosai.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel