Kannywood: Yadda Jarumi Adam A Zango Ya Auri Maimuna da Mata 6 daga 2007 zuwa 2025
- Amina Uba Hassan (Maman Haidar) ita ce matar Adam A Zango ta farko, kuma mabudin aure-aure bakwai da jarumin ya yi a shekaru 19
- A kaf cikin mata shida da ya aura kafin aurensa na bakwai a 2025, Zango ya ce rabuwa da Safiyya Chalawa ne ya jefa shi a damuwa
- A wannan rahoton, Legit Hausa ta kawo muhimman abubuwan sani game da mata bakwai da jarumi Zango ya aura daga 2006 zuwa 2025
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - A watan Agusta 2025, fitaccen jarumin Kannywood kuma mawaki Adam A. Zango ya sake shiga sabon babi na rayuwarsa ta aure.
Legit Hausa ta ruwaito cewa Adam A Zango ya angwance da amaryarsa Maimuna Musa, wadda aka fi sani da suna Salamatu a shirin Garwashi.

Source: Facebook
Mai shirya fim din Garwashi, Fauziyya D. Sulaiman, ta yi matukar murna da wannan auren, inda har ta nemi jin ra'ayoyin mutane kan jarumar da za ta maye gurbin Salamatu a shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hajiya Fauziyya ta shaida wa Legit Hausa cewa, irin wannan auratayyar tsakanin jarumai ne zai kara wa masana'antar kima a idon jama'a.
"Wannan abin so ne, kuma su duka biyun sun yi abin da ya dace. Muna yi masu addu'ar Allah ya ba su zaman lafiya, ya kawo zuriya ta gari."
- Fauziyya D. Sulaiman.
Game da shawarwarin da take ganin za ta iya ba ma'auratan, 'Uwar marayu' kamar yadda ake kiranta, ta ce:
'Ni shawara ta gare su baki daya shi ne su ji tsoron Allah, don shi aure ibada ne, idan aka rike shi a matsayin ibada, to za a ga daidai. Allah ya ba su zaman lafiya."
Wannan sabon aure na Adam A Zango ya sake jawo hankalin jama’a, musamman ganin yadda tarihin aurensa ya taba janyo cece-kuce a baya.

Kara karanta wannan
Lahadi: Ruwan sama da iska mai ƙarfi zai sauka a Abuja, Neja, Yobe da wasu jihohi
Zango: Jarumin da ya zarce sa'a a Kannywood
'Baba Ado' kamar yadda wasu a Kannywood ke kiransa, ya fara shahara tun farkon shekarun 2000, kuma tun daga lokacin ya gina kansa a matsayin ɗaya daga cikin manyan jarumai a fina-finan Hausa.
A cewar wani rahoton da aka wallafa a shafin Wikipedia, Adamu ya fito a fina-finai sama da 100, ya rera wakoki da dama, sannan ya kafa kamfaninsa na Zango Production.
Baya ga fim, Adam A Zango ya yi fice a waka da rawa, ya kuma lashe lambobin yabo da dama a harkokin nishadi a Arewa.
Wannan ya tabbatar da matsayinsa a matsayin jarumin da tasirinsa ya zarce Kannywood zuwa kasashen waje, domin ya sha fita waje yin wasanni.
Mata 7: Tarihin auren Adam a Zango
Tarihin aurensa shi ne mafi daukar hankali a rayuwarsa ta sirri. A cikin rahoton Daily Trust na 2022, an bayyana cewa ya yi aure sau da dama tun daga 2007.

Kara karanta wannan
Borno: Mayakan boko haram sun yi wa matafiya kwantan bauna, sun bude wa motarsu wuta
Legit Hausa ta tattaro bayanai game da mata 7 da Adam A Zango ya aura daga shekarar 2007 zuwa 2025:
1. Amina Uba Hassan

Source: Facebook
Amina Uba Hassan (Maman Haidar) ita ce matar Adam A Zango ta farko. An ce sun yi aure ne tun a shekarar 2007, kuma sun samu karuwar da namiji a 2008, Haidar.
Auren nasu bai jima suka rabu, kuma Amina ta nemi shawarar Adam A Zango kafin ta shiga harkar fim, inda a yanzu ta fito a fina finai masu yawa, ciki har da shirin Labarina.
A wata hira da ta yi a shirin Gabon's Room Talk Show na YouTube, Maman Haidar ta ce ta auri Adam A Zango ne a lokacin da ya dace, amma kuma 'na auri wanda bai dace ba, a lokacin da ya dace."
2. Aisha Muhammad daga Zaria
Bayan rabuwa da Amina, Adam ya kara aure da Aisha Muhammad, yar gari Shika da ke Zaria, jihar Kaduna.
An ruwaito cewa Aisha ta haifa wa Adam A Zango 'ya'ya uku, kafin Allah ya yi rabuwarsu bayan shekaru suna tare.
Rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da auren a matsayin wani bangare na jerin aure-auren da jarumin ya yi.
3. Maryam daga Nasarawa
Auren na uku da jarumin Kannywood din ya yi shi ne da wata Maryam, wacce aka ce 'yar asalin jihar Nasarawa ce.
An ce wannan auren na Adam A Zango bai wani jima ba, suka rabu.
4. Maryam AB Yola

Source: Facebook
Wata shahararriyar mace da ta shiga jerin matan jarumi Adam A Zango ita ce Maryam AB Yola, wadda aka daura aurensu a shekarar 2013.
Wannan aure ya dauki hankalin jama’a sosai saboda Maryam AB Yola ta kasance daya daga cikin 'yan matan Kannywood da ke tashe a lokacin.
Auren jaruman biyu ya mutu cikin ruwan sanyi ba tare da duniya ta ji ba. Amma duniya ta dauka a lokacin da aka ji Maryam ta yi wani auren.
A ranar 30 ga watan Satumba, 2022, jaridar Fim Magazine ta rahoto cewa Maryam AB Yola ta amarce da mijinta, Muhammad.
5. Ummul Kulsum daga Kamaru

Source: Facebook
A 2015, Zango ya auri Ummul Kulsum, wata kyakkyawar mace da aka ce asalinta 'yar Jamhuriyar Kamaru ce.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa Adam Zango ya auri Ummul Kulsum kasa da shekara uku da rabuwarsa da Maryam AB Yola.
Kafin auren Ummul Kulsum, Zango ya fuskanci zarge-zarge daga jaruma Rahama Sadau cewa yana yi mata tayin lalata, inda har ya cire ta daga wani fim dinta saboda ba ta amince ba.
Sai dai, Adam A Zango ya karyata wannan zargi, amma daga bisani ya ba jarumar da manajansa, Ali Nuhu hakuri.
Rahoto ya nuna cewa Ummul Kulsum ce ta haifa wa jarumi Zango 'yarsa ta fari, wacce aka sanya wa suna Murjanatu.
6. Safiyya Umar Chalawa daga Kebbi

Source: Facebook
A karshen watan Afrilun shekarar 2019, aka ruwaito cewa Adam A Zango ya auri matarsa ta shida, Safiyya Umar Chalawa, da aka fi sani da Suffy, 'yar jihar Kebbi.
Rahoto ya nuna cewa an daura auren Zango da Safiyya a karamar hukumar Gwandu ta jihar Kebbi, a masallacin Juma'a na fadar sarkin Gwandu.
Auren Suffy shi ne auren Zango na shida, bayan da aure biyar da ya yi a baya ya samar da yara biyar, maza hudu da mace daya.
A lokacin da ya sanar da auren, mun ruwaito cewa, jarumin ya yi alkawarin cewa ba zai sake ta ba, za ta kasance matarsa ta har abada.
Sai dai kuma, rahoton WikkiTimes ya tabbatar da cewa aurensu ya mutu a watan Afrilun 2023 bayan matsaloli na cikin gida.
Wannan rabuwar ita ce ta fi daukar hankali saboda Safiyya ta fito daga gida mai daraja, kuma rabuwar ta tayar da kura sosai a shafukan sada zumunta.
7. Maimuna Musa – sabon babi

Source: Facebook
A watan Agusta 2025, jarumi Zango ya yi aure karo na bakwai da Maimuna Musa (Salamatu a Garwashi). Wannan aure ya zo ne bayan shekaru biyu da rabuwa da Safiyya, kuma ya sake jawo cece-kuce a Kannywood.
Marubuciya, Uwa Aishatu Gidado ta taya su murna tare da yin nasiha, inda ta gargadi Maimuna kan tsoron Allah da girmama mijinta Zango.
Mun ruwaito cewa, Uwa Aishatu ta shawarci Zango ya rike amanar aure, ya rinka nuna kulawa ga amaryarsa, kuma wannan ya zama auren mutu-ka-raba.
Kalubalen da Adam A Zango ya fuskanta
A wata hira da aka yi da shi a Fabrairu 2024, Adam ya bayyana cewa ya fuskanci matsalar damuwa bayan rabuwarsa da Safiyya.
Ya ce wannan ya shafi aikinsa da rayuwarsa ta yau da kullum, abin da ya sa masoyansa da dama suka tausaya masa, kamar yadda muka ruwaito.
Jarumin ya kuma janye kalamansa na baya cewa ba zai sake aure ba, inda ya ce yana bukatar mace domin kare martabar iyalinsa.
Wannan ya nuna cewa duk da shahararsa, shi ma mutum ne kamar kowa da ke fuskantar ƙalubale a rayuwar aure da zamantakewa.
'Dalilin yawan mutuwar aure na' - Zango
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Adam A Zango, ya bayyana cewa, ba shi ne yake da sha'awar yin aure, yana sakin matansa ba, kaddararsa ce a hakan.
Fitaccen jarumin, ya ce Allah wannan tana daya daga cikin jarabawarsa ta rayuwa, yana mai danganta hakan da mukaddari daga Allah, abin da ba zai iya canja wa a karan kansa ba.
Adamu Zango ya yi nuni da cewa duk wani abu da ya roki Allah ya ba shi, ya samu, illa dai matar da zai aura, kuma su yi zaman aure ba tare da sun rabu ba.
Asali: Legit.ng





