Hotunan jarumin dandalin Kannywood tare da matarsa inda yake narkar da zuciyar ta da lakanin soyayya
- Hotunan fitaccen jarumin nan Adam A.Zango tare da uwargidansa Ummulkulsum
- Zango ya aure Ummulkulsum ‘yar kasar Kamaru a shekara ta 2015
- Jarumin ya sanya a shafinsa na kafar sada zumunta ta Instagram
Wadannan hotunan sun tabbatar da maganar Hausawa cewa soyayya ruwan zuma ce, kuma idan kuka kalli hotunan zaku tabbatar da hakan.
Fitaccen jarumin nan wanda kuka sani kuma mai shirya fina-fina na dandalin Kannywood Adam A.Zango ya kasa boye kaunar da yake da shi ga uwargidansa.
Legit.ng ta tattaro cewa, Prince Zango kamar yadda masoyarsa suka fi kiransa da shi ya sanya hotunansa tare da matarsa Ummulkulsum inda yake nakar da zuciyar ta a shafinsa na kafar sada zumunta ta Instagram.
Jarumin ya saci zuciyar matarsa tare da kalamai soyayya wanda ke sanya zukata murmushi.
KU KARANTA: Fina-finan Hausa da su ka ratsa gari a shekarar bara
Idan baku manta ba Zango dai ya auri Ummulkulsum wanda ‘yar asali kasar Kamaru ce cikin shekara 2015.
Wannan salon da kalamun nuna kauna wanda fitaccen jarumin ya nuna ga Ummulkulsum ya haifar da farin ciki ga masoyansa inda wasu da dama suna masa fatan alheri a shafinsa.
Abin da zamu ce shine Allah ya karo dankon kauna.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng