An daga daurin auren Adam Zango zuwa bayan karamar sallah

An daga daurin auren Adam Zango zuwa bayan karamar sallah

- Adam Zango ya bayyana daga daurin aurensa wanda za'ayi ranar juma'ar nan zuwa bayan sallah karama

- Ya bayyana hakan a shafinsa na Instagram, sannan ya yiwa dukkanin masoyansa godiya da fatan alkhairi

- Sai dai kuma jarumin bai bayyana dalilan da ya sa aka daga auren na shi ba

Shahararren dan wasan Hausan nan Adam A. Zango, wanda aka fi sani da Prince Zango ya daga shirinsa na kara aure a karo na shida, har zuwa bayan sallah karama.

A wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na Instagram a ranar Talatar nan da ta gabata da yamma, Zango ya sanar da daga bikin aure na shi, in da ya bayyana cewa: "Salam, 'yan uwa da abokan arziki, ina sanar da ku daga bikin aure na zuwa bayan karamar sallah. Zan sanar da ku sabon kwanan watan nan ba da dadewa ba."

An daga daurin auren Adam Zango zuwa bayan karamar sallah
An daga daurin auren Adam Zango zuwa bayan karamar sallah
Asali: Instagram

"Ga wadanda suke da niyyar halartar daurin auren na wa su dakata. Ina godiya sosai, Allah ya yi mana jagora." in ji shi.

Majiyarmu LEGIT.NG ta samu rahoton cewa Zango bai bayar da wani dalili na daga bikin auren na shi ba.

KU KARANTA: Ya kashe 'yan uwar budurwarshi su takwas saboda ta ce ba ta son shi

Idan ba a manta ba mun kawo muku rahoton cewa Zango ya gama shirye-shiryen bikin na shi tsaf, wanda zai yi a karo na shida, tun auren shi na farko da ya yi a shekarar 2006.

A rahoton da majiyarmu ta samu na nuna cewa Zango zai auri wata budurwa mai suna Safiya Umar Chalawa, wacce aka fi sani da Suffy, wanda za ayi da karfe 2:30 ranar Juma'ar nan.

Kafin a jinkirta auren, an so a daura auren a babban masallacin Sarkin Gwandu, da ke jihar Kebbi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng