Kannywood: Dalilin da ya sa nake auri-saki – Adam Zango

Kannywood: Dalilin da ya sa nake auri-saki – Adam Zango

Fitaccen jarumin nan na dandalin shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, Adam A Zango wanda aka fi sani da Prince Zango ya bayyana dalilin da ya sa yake yawan auran mata kuma daga bisani ya rabu da su.

Jarumin ya bayyana cewa ba wai baya iya zama da mace bane, sai dai "ba zan iya fada muku abin da ya hada shi da matata ta farko, da matata ta biyu da kuma matata ta uku ba."

“Allah yana hada mata, mace da namiji. Allah ya halicci mata domin su kasance ni’ima a garemu maza. Don mu Allah ya halicce su."

Adam ya kuma bayyana cewa Allah ya rigada ya tsara ma mutum kaddararsa da abunda zai faru da shi tun kan a haifasa har izuwa ranar da zai amsa kiran mahallicinsa.

Kannywood: Dalilin da ya sa nake auri-saki – Adam Zango

Kannywood: Dalilin da ya sa nake auri-saki – Adam Zango
Source: Twitter

Dan wasan ya bayyana hakan ne a hira da yayi da shafin BBC Hausa inda yake cewa: "Allah Ubangiji ya rubuta wa mutum abin da zai faru da shi tun daga farkon haihuwarsa har zuwa ranar mutuwarsa."

“Kuma wannan kaddarar da Allah yayi mun itace tawa, saboda ni , Allah yana gani, Allah ya ba ni komai da na roke shi, amma ban da mace wanda nake zaman aure da su.

KU KARANTA KUMA: Wani mutumi ya fasa lasifikar masallaci, saboda tana hana shi bacci a watan Ramadana

“Sannan kuma ina so na gayawa mutane wani abu cewa, duk mutin da ya kasance zai yi aure ya rabu da mace, ya kara yi kuma ya kara rabuwa da ita, toh ya kamata su gane cewa wannan mutumin ba mazinaci ba ne. Saboda ni Adamu Zango Allah ya ba ni, duk duniya a cikin masana’antar Kannywood, babu wanda mata ke so iri na. Toh me zan yi da aure?”

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Ga masu bukatar manhajar mu na Azumi a wannan wata mai albarka sai a bibiyi wannan shafi https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit

Mailfire view pixel