Aminu S Bono: Innalillahi, Fitaccen Darakta a Masana'antar Kannywood Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Aminu S Bono: Innalillahi, Fitaccen Darakta a Masana'antar Kannywood Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Allah ya yi wa shahararren darakta a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Aminu S Bono, rasuwa ranar Litinin 20 ga watan Nuwamba
  • Shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya tabbatar da rasuwar daraktan a shafinsa na soshiyal midiya
  • Ya yi addu'ar Allah ya gafarta masa kura-kuransa kuma ya sa Aljannah ta kasance makomarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kano - Fitaccen darakta kuma jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood, Aminu S Bono, ya riga mu gidan gaskiya.

Aminu S Bono ya rasu.
Aminu S Bono, Fitaccen Darakta a Masana'antar Kannywood Ya Rasu Hoto: Abba El-Mustapha1
Asali: Facebook

Abokin aikinsa kuma shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Abba El-Mustapha, ne ya tabbatar da rasuwar Daraktan a shafinsa na Facebook ranar Litinin.

Kara karanta wannan

Dalilai 4 da suka sa Anyanwu na PDP ya fadi zaben gwamnan Imo na 2023

El-mustapha ya kuma yi wa marigayin addu'ar samun rahamar Allah, inda ya yi fatan Allah ya sa Aljanna ta kasance makomarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A sanarwan da ya wallafa a shafinsa yau Litinin, 20 ga watan Nuwamba, 2023, Abba El-Mustapha ya ce:

"Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un, Allah ya yi wa shahararren darakta a Masana’antarmu ta Kannywood, Aminu S Bono rasuwa."
"Muna addu’ar Allah ya jikansa ya gafarta masa kura-kuransa, ya sa Aljanna ce makomarsa. Idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da kyau da imani."

Abokan aikinsa sun shiga jimami

Bayan samun labarin rasuwarsa, jaruman Kannywood da dama sun yi jimami tare da miƙa sakon ta'aziyya da addu'ar neman gafarar Allah ga marigayin

Ali Nuhu, sanannen jarumin Kannywood kuma darakta ya yi jimamin wannan rashi, yana mai cewa, "Allah ya jiƙanka da rahama Aminu, ya sa Aljanna ce makoma."

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon kwamishinan 'yan sanda a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya, Sifeta ya kadu

.

Fitacciyar jarumar nan, Momee Gombe, a shafinta na Instagram, ta yi wa Aminu Bono wanda ta kira da 'Babana' addu'ar Allah ya gafarta masa.

Aisha Izzar So ta yi magan kan rawar da take takawa a Fim

A wani rahoton kuma Aisha Najamu wacce aka fi sani da Aisha Izzar So ta bayyana matsayarta kan irin fina-finan da take fitowa.

A cewar ta dole ne a matsayinta na jaruma ta yi taka tsan-tsan kafin ta fito a cikin fim domin guje wa yin abin da ya ci karo da al'adarɓmutanen Hausawa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262