Dalilai 4 da Suka Sa Anyanwu Na PDP Ya Fadi Zaben Gwamnan Imo Na 2023

Dalilai 4 da Suka Sa Anyanwu Na PDP Ya Fadi Zaben Gwamnan Imo Na 2023

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amuran yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Imo, Owerri - A ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023, al'ummar jihar Imo suka fita mazabunsu sannan suka zabi dan takarar da suka fi so ya shugabance su na tsawon shekaru hudu masu zuwa.

Dalilan da suka sa PDP ta fadi zaben gwamnan Imo
Dalilai 4 da Suka Sa Anyanwu Na PDP Ya Fadi Zaben Gwamnan Imo Na 2023 Hoto: Senator Samuel Nnaemeka Anyanwu
Asali: Facebook

Gaskiyar dalilan da suka sa Anyanwu na PDP ya sha kashi a hannun Udodimma na APC a Imo

A zazzafar fafatawar da aka yi tsakanin mutum uku, Hope Uzodimma na APC mai mulki ya lallasa abokan hamayyarsa, Sam Anyanwu na PDP da takwaransa na LP, Athan Achonu kuma ya bayyana a matsayin wanda ya lashe zaben.

A ranar Lahadi, 12 ga watan Nuwamba, a Owerri, babban birnin jihar Imo, shugaban jami’ar tarayya ta Oye Ekiti, Farfesa Abayomi Fashina, wanda ya kasance baturen zaben, ya bayyana Uzodimma a matsayin wanda ya lashe zaben gwamna na 2023 a jihar Imo.

Kara karanta wannan

Cikakkun jerin jihohin da ke karkashin Ikon APC, PDP bayan zabukan Kogi, Bayelsa da Imo

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai wasu dalilai sun taka rawa wajen rashin nasarar PDP a zaben, wanda za a jero su a wannan labarin:

1. Rikicin PDP a jihar Imo

Kokarin son kwace mulki daga hannun APC da ganin sun samu nasara a zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba ya haifar da rikici a cikin jam’iyyar PDP.

A wani mataki da ya rutsa da shugabancin jam’iyyar, wasu jiga-jigan kwamitin ayyuka na jam’iyyar PDP na kasa a jihar Imo su bakwai sun yi murabus daga mukamansu da jam’iyyar.

Sun zargi Anyanwu da raina kokarin shugabannin na yiwa jam'iyyar aiki, suna masu cewa jam'iyyar PDP a Imo ta lalace ta yadda ba za a iya gyarata ba.

Haka kuma, manyan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP a jihar Imo sun sauya sheka zuwa wasu jam’iyyu kafin zaben.

Kara karanta wannan

Hukuncin kotun daukaka kara: Farfesan arewa ya yi gargadi kan yiwuwar barkewar rikici a Kano

Nasarar Anyanwu a matsayin dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP ya kara rura wutar rikicin da ke faruwa a jam’iyyar har ya kai ga ficewar manyan yan jam’iyyar.

Saboda haka, wannan ya taka rawar gani wajen kayen da PDP ya sha domin APC ta yi amfani da rikicin wajen cin riba a bangarenta.

2. Karfin iko na gwamna mai ci

Ba wai haka kawai Uzodimma ya samu zarcewa ba face saboda abubuwa da dama da suka yi aiki daidai a bangarensa.

Uzodimma, wanda ya rike kujerar sanata a yankin Imo ta Yamma sau biyu (yankin Orlu), ya samu nasara ta hanyar yin alkawarin dauko wanda zai gaje shi daga yankin Owerri, kuma shakka babu wannan ya yi masa aiki a zaben.

Sai dai kuma, Uzodimma bai tsuke bakin aljihu ba yayin da ya karbi hayar dukkanin otal a jihar Imo kwanaki kafin zaben. A tsarin da gwamnati ce ke kan gaba wajen kashe kudi a harkokin tattalin arziki, an fi samun riba idan aka hade da gwamnatin da ke karagar mulki.

Kara karanta wannan

"Yan maula sun fara": Jama’a sun yi caaa kan Ali Nuhu bayan ya taya Gawuna murnar nasara a kotun

3. Ikon tarayya

A halin yanzu dai Najeriya na ci gaba da tafiya kan tsarin jam’iyya daya. Jam’iyya mai mulki a jihar Imo da ta kasa ita ce APC.

Babbar jam’iyyar adawa a Najeriya ta samu rauni har a matakin tarayya domin wasu jiga-jigan jam’iyyar sun zama yan kanzagin Tinubu, wanda hakan ke kara yi wa PDP illa a matsayin mai adawa a siyasa. Hakan ne ya faru a jihar Imo daga sakamakon da aka tattara.

Gwamnatin tarayya ta shiga wasan yayin da Uzodimma ya gurgunta abokan hamayyarsa, ya buga kambun wasansu na sauya kwamishinan yan sandan jihar da kawo cikakken tsaro yayin zaben.

Rundunar soji da sauran hukumomin tsaro ma sun tsaya tsayin daka a jihar a lokcin zaben. Abokan hamayyarsa sun koka cewa an kawo sojoji don su taimaka wajen murda tsarin zaben.

4. Rashin tsaro da tashin hankali a Imo

A karkashin kulawar Uzodimma, jihar Imo ta zama matattarar rashin tsaro da tashe-tashen hankula. Sai dai wannan bai shafi damar da APC ke da shi a zaben ba, sai dai hakan ya yi sanadiyar da wasu suka gudu daga gidajensu kafin zaben wanda hakan ya rage damar PDP.

Kara karanta wannan

Dalilai 3 da suka sa Timipre Sylva na APC ya sha kaye a zaben gwamnan Bayelsa

Jigon NNPP kan tsige Abba

A wani labarin, mun ji cewa Adekunle Razaq Aderibigbe, jigon jam'iyyar NNPP a jihar Lagas, ya bayyana hukuncin kotun daukaka kara da ta tsige Gwamna Abba Yusuf a ranar Juma'a, 17 ga watan Nuwamba, a matsayin "wani yunkuri na yiwa masu rinjaye fashi".

Da yake zantawa da jaridar Legit a wata hira da shi a ranar Asabar, 18 ga watan Nuwamba, Aderibigbe ya fusata da hukuncin kotun.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng