Bidiyon Shigar Damisa Wurin Shakawata ya Firgita Jama'a, Sun yi Martani

Bidiyon Shigar Damisa Wurin Shakawata ya Firgita Jama'a, Sun yi Martani

  • Bidiyon wata damisa yayin da take kokarin shiga wani wurin shakatawa a kudancin Afirka ya jawo cece-kuce a soshiyal midiya
  • Dabbar mai hatsarin gaske ta shiga zuwa bangaren cin abinci a wurin, inda mutane ke zaune suna cin abinci, wanda hakan ya firgita masu amfani da yanar gizo
  • Mutane sun firgita da faifan bidiyon, inda jama'a da dama suka ce da suna wurin kururuwa za su yi yayin da suka yi arba da damisar

Abun da ba a saba gani ba na yadda damisa ke takawa cikin mutane ya ba jama'a a yanar gizo firgici mara misaltuwa. A wani bidiyo da @jacog9 ya wallafa a TikTok, an hango sarkin gudun yana kalle cikin wajen shakatawar ba tare da kaiwa kowa farmaki ba.

Damisa wurin shakatawa
Bidiyon Shigar Damisa Wurin Shakawata ya Firgita Jama'a, Sun yi Martani. Hoto daga @jacog9/TikTok
Asali: UGC

An ga bakin a natse a gaban dabbar mai matukar hatsari kamar sun saba da shi.

Kara karanta wannan

Kyakyawar Baturiya Ta Tafi Da Saurayinta Dan Najeriya Kasarsu Don Ya Gana Da Danginta, Bidiyon Ya Kayatar

Guntun bidiyon bai bayyana yadda abun ya karashe ba, amma bidiyon mai dakiku kadan ya janyo hankalin dubbannin jama'a a yanar gizo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Martanin masu amfani da soshiyal midiya

Masu amfani da yanar gizo sun yi ba'a kan yadda 'yan Afirka cewa ba za su taba karyata zargin da sauran sassan duniya cewa muna rayuwa da dabbobi masu hatsarin gaske a koda yaushe.

@king_varish21 tayi ambato:

"Idan duniya ta tambayi ko da gaske ne idan muna rayuwa cikin dabbobi zan tura musu wannan."

@wendyjansevanrens ya ce:

"Idan wani ya kara tambaya na ko zakuna da damisoshi na yawo a titina, zan tura musu wanan bidiyon."

@tsheps_snie yayi tsokaci:

"Ba zai taba zama ni ba."

@lolo_v27 yayi ambato:

"Hakan yayi kama da yadda budurwa ke hanzarin zuwa kare tsohuwa ba tare da kasa a guiwa ba, kyan zuciya."

Kara karanta wannan

Sabon Salo: Wata Amarya Ta Yi Amfani da Maza 5 a Matsayin Kawayenta Ranar Biki, Bidiyon Ya Ja Hankali

@vick.32 ya kara da cewa:

"Kyawun kasarmu, abun takaici shi ne yadda akwai kusa da kowanne titi a wannan gwamnatin."

@zeema_05 ta ce:

"Amsar ita ce Eh, A Afirka, muna yawo tare da zakuna da damisoshi a titinan mu."

@udboybt yayi tamabaya:

"Meyasa babu wanda ke gudu ne?"

@zentandostudio ya ce:

"Yadda kuke gwada ikon Ubangiji bayan taba iyawa ba."

Bidiyo tsohuwar da ta girma cikin birai, tace a cikinsu ta ke samun natsuwa

A wani labarai na daban, wata tsohuwa ta bayyana tana bada labarin yadda ta girma a cikin birai dukkan rayuwarta.

Ta sanar da yadda aka sace ta kuma ta koma rayuwa a cikin birai wanda a halin yanzu cikinsu kawai ta ke samun natsuwa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel