Rigimar PDP: Gwamnonin Kudu Sun Yanke Shawara, Zasu Mara Wa Atiku-Okowa Baya a 2023

Rigimar PDP: Gwamnonin Kudu Sun Yanke Shawara, Zasu Mara Wa Atiku-Okowa Baya a 2023

  • Gwamnonin jam'iyyar PDP na yankin kudu maso kudu sun gana a Bayelsa amma an nemi Wike an rasa
  • A zaman tattaunawar da suka yi ranar Laraba, gwamnonin sun jaddada matsayarsu ta goyon bayan Atiku/Okowa
  • A cewarsu sun zaɓi zuwa Bayelsa ne domin jajantawa ɗan uwansu wanda jiharsa ta sha fama da matsalar ambaliya

Bayelsa - Gwamnonin jam'iyyar PDP na shiyyar kudu maso kudancin Najeriya sun gana a Yanagoa, babban birnin jihar Bayelsa ranar Laraba 23 ga watan Nuwamba, 2023.

Channels tv ta ruwaito cewa a wannan zama gwamnonin sun yanke shawarin goyon bayan ɗan takarar jam'iyyarsu, Atiku Abubakar, da abokin takararsa, Ifeanyi Okowa.

Gwamnonin PDP a kudu maso kudu.
Rigimar PDP: Gwamnonin Kudu Sun Yanke Shawara, Zasu Mara Wa Atiku-Okowa Baya a 2023 Hoto: channelstv
Asali: UGC

Gwamnonin da aka hanga sun halarci taron sun haɗa da Godwin Obaseki na Edo, Ifeanyi Okowa na Delta, Udom Emmanuel na Akwa Ibom da mai masaukin baki Duoye Diri na jihar Bayelsa.

Kara karanta wannan

Tinubi Ya Yi Gagarumin Rashi, Wani Shugaban APC da Wasu Jiga-Jigai Sun Fice Daga Jam'iyyar

Legit.ng Hausa ta fahimci cewa gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas bai halarci taron ba kuma hakan ba zai rasa alaƙa da rashin zaman lafiya a jam'iyyar PDP ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wike dai na jagorantar tawagar gwamnonin G5 da suka nuna fushinsu kan haɗa ɗan takarar shugaban ƙasa da kuma shugaban jam'iyya na ƙasa duk 'yan arewa.

Tawagar G5 sun jima suna nanata bukatar sauke Iyorchia Ayu daga matsayinsa da kuma maye gurbinsa da ɗan kudu a matsayin sharaɗin zaman lafiya a cikin gida.

Wane mataki gwamnonin suka ɗauka a taron?

Da yake hira da 'yan jarida bayan kammala taron, Gwamna Obaseki na Edo yace sun zauna ne domin nuna goyon bayansu ga tikitin Atiku/Okowa yayin da ake tinkarar zaɓen 2023.

Ya ƙara da cewa sun zaɓi haɗuwa a Bayelsa ne domin su jajantawa takwaransu wanda jaharsa ta sha fama da Ibtila'in ambaliyar ruwa a baya-bayan nan, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Ɗan Takarar Shugaban Kasa, Kwankwaso Ya Dira Patakwal Wurin Gwamna Wike

Obaseki yace:

"Muna da ƙungiyar gwamnonin kudu maso kudu kuma ɗan takarar mataimaki Okowa ne shugaba, mun zaɓi zuwa nan Bayelsa ne don jajantawa abokin aikinmi bisa jarabawar ambaliyar da suka sha fama da ita."
"Mun samu damar tattauna wasu batutuwa gabanin zuwan babban zaɓe. Mun kuma samu damar jin halin da ake ciki a matakin ƙasa daga ɗan uwanmu Okowa, ɗan takarar mataimakin shugaban kasa."
"Haka zalika mun jaddada cikakken goyon bayanmu ga takarar Atiku Abubakar kuma mun tabbatar masa muna nan tare da shi."

A wani labarin kuma Babbar Kotun tarayya ta yi watsi da ƙarar da wata jam'iyya ta shigar da Bola Tinubu, ɗan takarar APC a 2023

A ranar Litinin, 21 ga watan Nuwamba, 2022 Kotun tace waɗanda ke ƙara basu ɗauki lamarin Kotu ta muhimmanci ba don haka ba dalilin cigaba da shari'ar.

Jam'iyyar APC tare da haɗin guiwar wasu sun gurfanar da INEC, Tinubu, da APC bisa tuhumar ɗan takarar shugaban ƙasan ya ba da bayanan karya game da karatunsa.

Kara karanta wannan

Wike da Sauran Gwamnonin G-5 Sun Kafa Sabuwar Kungiya, Sun Ce Sam Ba Zasu Taya Atiku Kamfen Ba

Asali: Legit.ng

Online view pixel