Mari mai kwance kunne: Sabon bidiyo ya nuna yadda matar Obiano ta takali fadan Bianca Ojukwu

Mari mai kwance kunne: Sabon bidiyo ya nuna yadda matar Obiano ta takali fadan Bianca Ojukwu

  • Bayyanar wani bidiyo a shafin yanar gizo ya sanya an sake waiwayan rikicin da ya afku tsakanin matar tsohon gwamnan Anambra Ebelechukwu Obiano da Bianca Ojukwu a Maris
  • A cikin sabon bidiyon, an gano lokacin da Ebele ta tashi ta je har wajen da Bianca ke zaune a wajen taron rantsar da Soludu sannan ta dungure mata kai
  • Ita kuma hakan ya bata mata rai inda a nan take ta dauketa da mari kafin aka shiga tsakaninsu

Anambra - Wani sabon bidiyo ya bayyana a yanar gizo kan rikicin da ya wakana tsakanin matar marigayi Odumegwu Ojikwu, Bianca da matar tsohon gwamnan jihar Abia, Ebelechukwu Obiano, a wajen bikin rantsar da Farfesa Charles Soludo.

Bidiyon wanda Bianca ta wallafa a shafinta na Facebook ya kuma nuno lokacin da uwargidar tsohon gwamnan ta isa wajen da take zaune a yayin taron.

Kara karanta wannan

Bauchi: An Kama Mai Hidimar Ƙasa Na Bogi Ya Saci Wayoyi a Sansanin NYSC

Mari mai kwance kunne: Sabon bidiyo ya nuna yadda matar Obiano ta takali fadan Bianca Ojukwu
Mari mai kwance kunne: Sabon bidiyo ya nuna yadda matar Obiano ta takali fadan Bianca Ojukwu Hoto: Bianca Odumegwu Ojukwu
Asali: Facebook

Da isarta wajen da Bianca take, sai ta takale ta da fada ta hanayar dungure mata goshi tana zaginta.

Bianca wacce hakan bai yi mata dadi ba sai ta mike sannan ta sharara mata mari. Jim kadan bayan nan sai mutane suka shiga tsakani inda suka raba su sannan sai Ebele ta koma wajen zamanta.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A yanzu haka, Ebele na takarar kujerar sanata a babban zabe mai zuwa.

Kalli cikakken bidiyon a kasa:

Matar Tsohon Shugaban Biafra Ta Faɗi Dalilin Da Yasa Ta Shararawa Matar Gwamna Mai Barin Gado Mari

A baya mun ji cewa ambasada Bianca Ojukwu, matar marigayi Cif Chukeuemeka Ojukwu, ta bayyana abin da ya faru tsakanin ta da tsohuwar First Lady ta Jihar Anambra, Ebelechukwu Obiano.

Yayin taron rantsuwar kama aiki na Gwamna Charles Soludo, a ranar Alhamis, Ebelechukwu Obiano da Bianca sun yi rikici. Lamarin ya janyo hankulan yan Najeriya da dama a dandalin sada zumunta.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Matar gwamnan APC ta shiga jerin 'yan takarar sanata a jiharsu

Daga bisani Soludo ya nemi afuwar al'ummar Anambra da bakin da suka hallarci taron, yana mai cewa rashin jituwa ne tsakanin mutanen biyu ya janyo hakan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel