Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

Yadda za a gwabza wajen zaben fitar da ‘dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC

  • Nan ba da dadewa ba jam’iyyar APC mai mulki za ta gudanar da zaben fitar da gwani a Najeriya
  • Ana sauraron a ga wanene wanda zai rikewa jam’iyyar tuta a takarar shugaban kasa a zaben 2023
  • Daga cikin masu neman tikiti a APC akwai Bola Tinubu, Yemi Osinbajo da kuma Rotimi Amaechi

Legit.ng Hausa ta yi sharhi a game da yadda siyasar cikin gidan jam’iyyar APC mai mulki za ta kasance wajen fitar da ‘dan takarar shugaban kasa.

Mun bi wasu daga cikin manyan ‘yan takarar, mun duba inda suke da karfi, da inda suka gaza.

1. Bola Tinubu

Asiwaju Bola Tinubu ya dade ya na harin tikitin zama shugaban kasa a APC. ‘Dan siyasar ya na cikin wadanda suka fi kowa mabiya da kafa mutane a jam’iyya.

Kara karanta wannan

Sai dai kai ka zo: Tinubu ya tura gayyata ga gwamnonin APC, suka ki amsa gayyatarsa

Tinubu bai tare da wasu Gwamnoni musamman bayan hana Akinwumi Ambode da Godwin Obaseki tazarce a lokacin da APC ta ke hannun Adams Oshiomhole.

Sai dai Legit.ng Hausa ta fahimci mafi yawan gwamnonin Kudu maso yamma su na goyon bayan Tinubu. Haka zalika a Arewa yana tare da irinsu Abdullahi Ganduje.

Jihohin Kano da Legas sun fi ko ina yawan kuri’u a Najeriya. Idan har za ayi zaben ‘yar tinke, wannan zai ba Tinubu dama a kan sauran masu neman takara a APC.

Masu ja da Tinubu a yankin Yarbawa sun hada da tsofaffin yaransa; Dr. Kayode Fayemi da Rauf Aregbesola, da irinsu Gwamnan jihar Ondo, Rotimi Akeredolu SAN.

Manyan ‘yan siyasan da ta ke da ta-cewa a yankunansu irinsu Sanata Kashim Shetima da Sanata Abu Ibrahim su na ganin Tinubu ya dace a damkawa mulki a 2023.

Kara karanta wannan

Atiku, Saraki da Tambuwal sai sun dage, ‘Yan takarar Kudu sun hada-kan su a PDP

2. Yemi Osinbajo

Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana niyyar shiga takarar shugaban kasa a APC. Amma mataimakin shugaban kasar bai da wani karfi a siyasar cikin gidan jam’iyyar APC.

Duk da haka, Osinbajo zai iya samun tikiti a APC idan shugaban kasa yana tare da shi. Abin zai iya zuwa masa da sauki idan akalla ya na tare da wasu gwamnonin jihohi.

Alamu na nuna akwai wasu daga cikin hadiman shugaban kasa da suke goyon bayan Osinbajo ya samu tikiti domin ya gaji Muhammadu Buhari, nan gaba kadan za a gani.

Shugabannin jam’iyyar APC
Shugaban kasa, Shugaban APC da Mala Buni Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

3. Rotimi Amaechi

A makon da ya wuce Ministan sufuri na kasa, Rotimi Amaechi ya ayyana burin takarar shugaban kasa. Wasu na ganin ya na tare da wasu kusoshi a fadar Shugaban kasa.

Ko da Amaechi ya yi baba-kere a APC ta jihar Ribas, bai da karfi sosai a uwar jam’iyya. Ba a ga wasu manyan da ake ji da su a APC a bikin kaddamar da takararsa ba.

Kara karanta wannan

Shirin 2023: Kwankwaso ya koma NNPP, ta yiwu Tinubu kuma ya koma SDP, inji majiya

Idan Ministan ya samu goyon bayan wasu daga cikin Gwamnonin APC na Arewa maso yamma, ana tunanin sai an yi da gaske za a tika shi da kasa a zaben tsaida gwani.

4. Yahaya Bello

Kusan dai shi kadai yake rawarsa, kuma yake tsallensa a jam’iyyar APC. Mafi yawan ‘ya ‘yan APC su na ganin 2023 lokaci ne da ‘dan kudu zai rike tutar shugaban kasa.

Zuwa yanzu Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello ne fitaccen ‘dan Arewa da yake harin tikitin APC. A yadda abubuwa suke tafiya, da wahala gwamnan ya iya kai wani labari.

5. ‘Yan siyasar Ibo

Daga cikin masu neman shugaban kasa daga kudu maso gabas a APC akwai Rochas Okorocha, Orji Uzor Kalu, da David Umahi wanda ya na cikin sababbin shiga APC.

Ana rade-radin Chris Ngige da Ogbonnoya Onu za su nemi takarar shugaban kasa a APC. Onu ya nemi takara a zaben 1999, haka zalika Ngige ya na cikin manyan jam’iyya.

Kara karanta wannan

PDP ta na fuskantar barazana a jihohin Kudu idan ta ba Atiku, Saraki ko Tambuwal takara

Jam’iyyar APC ba ta da karfi sosai a kudu maso gabas, watakila hakan za isa ‘yan siyasar yankin su hada-kai, domin su tsaida wani mutum daya a matsayin ‘dan takararsu.

Matsayar kusoshin APC

Wanene ‘dan takarar Shugaban kasa?

Mai girma Muhammadu Buhari da aka yi wata hira da shi, ya nuna cewa akwai wanda yake so ya gaje shi, amma bai bayyanawa Duniya sunansa ba, ya bar jama’a a duhu.

Duk masu neman tikitin APC su kan yi zama da shugaban kasar kafin su ayyana burin takararsu, har yau babu wanda ake da labarin ya na tare ko bai tare da shugaban kasar.

Wanene ‘dan takarar Gwamnoni

Kusan har yanzu ba za a iya cewa ga wanda gwamnonin APC su ke tare da shi ba. Asali ma zai yi wahala kan gwamnoni 22 ya hadu, amma dai su na da ta-cewa a jam’iyya.

Wanene ‘dan takarar ‘yan majalisa

Ana ganin Bola Tinubu ne ya kawo shugaban majalisa dattawa (Ahmad Lawan) da shugaban majalisar wakilai (Femi Gbajabiamilla) kan kujerun da suke kai a yau.

Kara karanta wannan

Neman kujerar Shugaban kasa ya barka Atiku, Saraki da ‘Yan takarar PDP, kai ya rabu 3

Amma kuma ba dole ba ne a ce Tinubu na da iko ga zabin duka ‘ya ‘yan APC a majalisar tarayya. Gwamnoni su na da iko a kan ‘yan majalisa da suka fito da jihohinsu.

Sabon shugaban jam’iyya

A watan Maris ne APC ta zabi sabon shugaban jam’iyya, Abdullahi Adamu. Tsohon Sanatan ya na cikin wadanda ba su ganin dole ne sai mulki ya koma kudu a zaben 2023.

A doka, akwai hanyoyi uku da za a iya bi wajen fito da ‘dan takara. A ba duk ‘dan jam’iyya kuri’a, ko ayi tsarin ‘ya ‘yan delegate ko a nemi yin maslaha tsakanin 'yan takara.

Nan da watan Mayu ake sa ran za a san wanene zai zama 'dan takarar shugaban kasa a APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel