Mijin Status: Yadda budurwa ta ga saurayi a WhatsApp, ta san yadda ta aure shi

Mijin Status: Yadda budurwa ta ga saurayi a WhatsApp, ta san yadda ta aure shi

  • Wata ‘yar Najeriya ta kamu da son wani mutum ta hanya mai ban mamaki, kuma lamarin ya kare a wani aure mai ban shauki wanda ya taba zukatan mutane da dama
  • Budurwar ta ce mutumin da ta aura amsar addu’arta ce ta sirri da ta dade tana yi, kuma mutane da yawa sun sha mamakin haka
  • Ta hadu da mijin nata ne a lokacin da ta kulla hadi da wani mutum cewa ya shaidawa mijin nata tana son za ta aure shi

Wata ‘yar Najeriya ta ga hoton wani kyakkyawan matashi da wani ya yada a kafar WhatsApp. Nan take ta harbu da sonsa, sannan ta kulla hanyar neman ta aure shi ta huta, wanda daga baya kwatsam aka ga hotunan aurensu.

Ba ta tuntube shi kai tsaye ba. Sai kawai ta aika da sako gareshi ta hanyar wani, wanda ya shaida mata a mutumin bai da aure.

Kara karanta wannan

Ya taro 'Match': Bidiyon tashin hankali yayin da mai tura kuran ruwa ya kwarzane mota Benz

Yadda ta aure saurayi daga Status
Mijin Status: Yadda budurwa ta ga saurayi a WhatsApp, ta san yadda ta aure shi | Hoto: @Okiki_hurla
Asali: UGC

A fada masa ina sonsa zan aure shi

Sakon da ta aika sako ba dokon surutu bane, sako ne masu dauke kalmomi kadan amma masu citta, domin su suka narkar da zuciyarsa har ya amince.

Sakon da ta tura shi ne:

'A fada masa ina son aurensa. Sannan a nuna min martaninsa".

Mutumin da zai isar da sakon ma sai da ya gyagyata da dariya, amma burinta ya cika kuma ta shiga shafin Twitter don bayyana murnarta.

Martanin 'yan Twitter

'Yan Twitter sun mayar da martani kan wannan abu mai ban shauki. Ga kadan daga cikin martaninsu:

@Pharm_chocolate ya ce:

"Mata ku san hannunku! Ina taya ku murna."

@Nickib900 ya mayar da martani:

"Na tayaki murna, amma yanzu samari sai girman kai idan kayi musu magana kai kwambo kawai."

Kara karanta wannan

Tsadar fom din takara: Ana son hana matasa mulki a Najeriya, inji wani dan takaran APC

@Xtopher_Uzo ya ce:

"'Yan mata kun gani, yanzu ta mutu? Duniya ta kare ne?"

@KUNLEADEIGBE yayi sharhi da cewa:

"Haka ake yi..... ba wai shirmen jiran kofa ba, ki bishi ki mallaki abin ki, na dai taya ki murna."

Kwalliya iya kwalliya: Ma'abota kafafen sadarwa sun tofa albarkatun bakinsu kan kwalliyar Amarya

A wani labarin, farashin kudin kwalliyar zamani da ake yiwa amare da kawayensu na farawa daga N5000 zuwa N100,000, dangane da mai kwalliyar da irin kayan da akayi amfani.

Amma wasu masu sana'ar kwalliyan kan shiga uku idan suka tafka kuskure musamman kan amare.

Da alamun irin haka ya faru a wani bidiyon da ya bazu a soshiyal midiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.