Bana yi kuma: Budurwa ta soke aurenta ana saura kwana 3 saboda sun samu sabani da angon nata

Bana yi kuma: Budurwa ta soke aurenta ana saura kwana 3 saboda sun samu sabani da angon nata

  • Wata matashiya yar Najeriya, Ada Uburu ta soke aure tsakaninta da sahibinta ana saura kwanaki uku bikin nasu
  • Ada ta bayyana cewa ta soke auren ne saboda mai shirin zama angon nata yana yawan dukanta harma yana kokarin raba ta da numfashinta
  • Budurwar ta kuma baiwa yan uwa da abokan arziki hakuri a kan wannan matakin da ta dauka don tsiratar da rayuwarta

Wata budurwa mai suna Ada Uburu ta soke aurenta da masoyinta David Okike, saboda rikicin cikin gida da ya gibta a tsakaninsu, shafin Linda Ikeji ya rahoto.

Matashiyar ta bayyana cewa mai shirin zama angon nata ya fara cin zarafinta ne tun bayan da ya biya kudin sadakinta, inda ta kara da cewar ta dade tana shanye bakin ciki a tattare da soyayyarsu da nufin abubuwa za su daidaita.

Kara karanta wannan

Ko Buhari ya sauka matsalar tsaro ba za ta kare ba, Fadar Buhari ga dattawan Arewa

Bana yi kuma: Budurwa ta soke aurenta ana saura kwana 3 saboda sun samu sabani da angon nata
Bana yi kuma: Budurwa ta soke aurenta ana saura kwana 3 saboda sun samu sabani da angon nata Hoto: Linda Ikeji
Asali: UGC

Kamar yadda aka tsara tun farko, za a daura auren ne a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilu 2022, a garin Amenu Uburu, jihar Ebonyi.

Yana jibga ta da zaran na dan bata masa rai

Ada ta bayyana cewa akwai lokacin da saura kadan mai shirin zama mijin nata ya kasheta ba don yan uwa da makwabta sun gaggauta shiga Tsakani ba.

Shafin Vanguard ya rahoto cewa a wani wallafa da matashiyar ta yi, ta bayyana cewa:

“A ranar Litinin na makon da ya gabata, kawai don wani dan sabani ya gibta tsakaninmu sai ya yi mun mugun duka sannan ya shiga madafar mahaifiyarsa da gudu domin daukar adda.
“Da na lura cewa makami zai dauko, sai na rufe kofa wanda yasa ya fasa shigowa.

Kara karanta wannan

Yaudara da neman goyon baya: Martanin Shehu Sani kan ikirarin Osinbajo na bin sahun Buhari

“Mahaifiyarsa da yan uwansa mata da wasu makwabta suka dungi rokonsa da kada ya yanke ni da addan.
“Na gaji da wadannan abubuwan da ke faruwa.
“Na soke aure tsakanina da David Okike wanda ya kamata ayi a ranar Asabar, 16 ga watan Afrilun 2022.
“Dan Allah, yan uwana da abokaina, ku yi hakuri da wannan bata maku da nayi.
“Dan Allah, ku mutunta zabina. Nagode kuma Allah ya yi maku albarka dukanku.”

Katin gayyata 20 muka buga, mun samu 500k, Amarya da angon da suka yi karamin biki

A wani labarin, bayan kauda kai daga kashe-kashen kudi da tada kurar da aka san yawancin 'yan Najeriya nayi a shagulgulan bikinsu, wasu ma'aurata sun yanke shawarar yin aure ta hanyar hada karamin liyafa.

Ademola Adebusoye da masoyiyarsa, Titilope Adebusoye, sun yi aure a 2020 a Legas, sannan ya bayyana farin cikinsa na yadda suka yi dan kwarya-kwaryar shagali, inda ya shawarci masoya a wata wallafa da ya yi cikin kwanakin nan da sun yi abunda zasu iya.

Kara karanta wannan

Ramadan: Magidanci ya lakada wa matarsa mai ciki mugun duka kan abincin Sahur

Ademola ya bayyana yadda suka yi dan kwarya-kwaryar shagalin biki yayin tattaunawa da Legit.ng, inda Ademola ya ce lokacin sun yi niyyar yin aure, amma basu da kudin daukar ragamar bikin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel