Daga karshe: Naziru ya yi bayani, ya ce ya tattauna da jaruman Kannywood, sun yi sulhu

Daga karshe: Naziru ya yi bayani, ya ce ya tattauna da jaruman Kannywood, sun yi sulhu

  • An dinke barakar da ta barke tsakanin jaruman fim din Hausa na Kannywood a cikin makon nan saboda wasu maganganu
  • An samu sabani tsakanin jaruman Kannywood kan batun yadda furodusoshi ke biyan kudi kan fina-finai
  • A yanzu dai Naziru Sarkin Waka ya ce an zauna da jaruman, an tattauna da juna an kuma samu mafita daga karshe

Kano - Bayan da aka sha fama a tsakani, tare da luguden maganganu da cece-kuce a masana'antar Kannywood a makon nan, an samu dakyar kura ta lafa.

Cece-kucen da ya dauki kwanaki biyu ana fama ya faro tun lokacin da BBC ta yi hira da wata dattijuwar jarumar fim, inda ta fadi yawan kudin da ake biyan jarumai.

Hoton bayan tattaunawar 'yan Kannywood
Daga karshe: Naziru ya yi bayani, ya ce ya tattauna da jaruman Kannywood, sun yi sulhu | saheliantimes.com
Asali: UGC

Batun ta ya jawo cece-kuce, lamarin da ya kai ga sabani tsakanin wasu 'yan fim har ta kai ga duniya ta ji wasu daga cikin sirrukansu.

Kara karanta wannan

Sauki ya samu: Sabbin hotuna da bidiyon Maryam Yahaya a kasar Dubai

Alhamdulillah, an tattauna, an samu matsaya

Cikin daren ne Naziru Sarkin Waka ya yada wasu hotuna a shafinsa na Instagram, inda ya bayyana cewa jaruman sun zauna an yi gyaran da ya dace.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

A karkashin hotunan, ya yi jawabin sulhun, inda ya hada da yin addu'o'in samun zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin jaruman.

Hakazalika, ya roki Allah ya sanyawa zaman da suka yi albarka ya kuma daukaka Muslunci da Musulmi.

Rubutun Naziru a shafin Instagram ya ce:

"Alhamdulillah mun zauna kuma mun fahimci juna kuma mun gyara duk abunda ya kamata mu gyara mun fahimci juna…. Muna kuma rokon Allah ya sakawa zaman namu albarka amin :pray::skin-tone-6: Allah ya taimaki musulinci da musulmi ya kuma hada kawunan mu ya sakawa da shugabannin mu da alkairi amin."

Kalli hotunan:

Kungiyar MOPPAN ta gargadi yan Kannywood da su daina kwancewa juna zani a kasuwa

Kara karanta wannan

Babu dan fim da ya tumbatsa duniya ta san shi da zai ce iya kudin fim ke rike shi – Rukayya Dawayya

A wani labarin, kungiyar masu shirya fina-finan Hausa ta Najeriya (MOPPAN), ta gargadi yan wasan Kannywood da su daina kwancewa junansu zani a kasuwa musamman a shafukan soshiyal midiya.

Wannan jan kunnen ya biyo bayan rikicin da ya kunno kai a masana’antar cikin yan kwanakin da suka gabata.

A wata sanarwa dauke da sa hannun kakakinta, Al-Amin Ciroma, kungiyar ta ce ta ga akwai bukatar takawa yan wasan birki ne a yayin da ake ci gaba da kace-nace dangane da rigingimun da suka biyo bayan tattaunawar da BBC Hausa ta yi da Hajiya Ladin Cima.

Asali: Legit.ng

Online view pixel