Yadda Inyamurin Najeriya ya auri Musulma yar kasar Malaysia
- Wani Inyamuri dan Najeriya yayi gwaninta inda ya auro mata musulma yar kasar Malaysia
- Yan uwan amaryar da abokan ango duk sun halarci taron daurin auren
Soyayya ruwan zuma, kamar yadda Hausawa ke fadi, kuma dama ai matar mutum kabarinsa, kamar haka ne wani rahoto da Legit.ng ta samu dake nuna tsananin soyayyar data shiga tsakanin wasu masoya biyu mabiya addinai daban daban kuma yan kasa da kabila daban daban.
Wasu hotunan dake ta yawo a shafukan kafafen sadarwa sun nuna yadda wani dan Najeriya daga kabilar Inyamurai ya auri wata kyakkyawar yarinya musulma 'yar kasar Malaysia.
KU KARANTA: Buratai ya jagoranci bikin ƙaddamar da sansanin sojoji a Daura
Wannan Inyamuri mai suna Collins, ya auri budurwar tasa ne a ranar Asabar 20 ga watan Mayu, inda aka daura auren nasu a gundumar Jasin dake garin Melaka a kasar ta Malesiya.
A cikin hotunan an hangi yan uwan amaryar Collinsa tare da yan’uwa da abokan angon duk sun halarci taron daurin auren.
Mu a anan sai dai muce Allah ya bada zaman lafiya.
Ga sauran hotunan nan:
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Yan mata sun bayyana nawa suke son namiji su ya mallaka kafin su aure shi
Asali: Legit.ng