Ga wata yarinya da aka haifa sau biyu a duniya

Ga wata yarinya da aka haifa sau biyu a duniya

– LynLee wata jinjira ce da aka Haifa sau biyu a rayuwa

An fito da ita daga mahaifa anyi mata aiki, sannan aka kara maida ta ciki

Sai can daga baya aka kara haihuwar wannan yarinya

Ga wata yarinya da aka haifa sau biyu a duniya

Wani abin ban al’ajabi ya faru a duniya, wanda kusan ba a taba jin irin sa ba, CNN ta kawo labarin wata jinjira mai suna LynLee Hope, wanda aka haifa sau biyu. Da fari an fito da wannan yarinya tana ciki, aka yi wani aiki, sannan kuma aka kara maida ta cikin mahaifiyar ta inda ta koma tayi zaman ta, sai daga baya aka kara haihuwar ta.

KU KARANTA: Shekearu goma da nada Sarkin Musulmi

Yayin da wannan jinjira ta ke makonni 23 a duniya, an fito da ita daga mahaifa, bayan an gane cewa tana da wata cuta, aka yi mata aiki, sannan aka maida ta cikin mahaifa inda ta kara zaman ta na makonni 36 a ciki, can daga baya aka haife ta tana jinjira ‘yar wata tara.

Da mahaifiyar jinjirar ta ke bayanin abin da ya faru, tace Likitoci sun bayyana masu cewa yarinyar da za a haifa tana da matsala a wajen duburar ta, don haka aka yi maza aka fito da ita aka yi mata aiki, aka kuma maida ta ciki.

Dakta Darell Cass, wanda shine Darektan Asibitin da aka yi wannan aiki a Texas, yace akan samu irin wannan matsalar musamman a yara mata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel