Zaben Kasar Jamus da aka kammala jiya: 'Yan Kasar Jamus Basa Zaben Shugaban Kasa Kai tsaye, duba nasu tsarin zaben

Zaben Kasar Jamus da aka kammala jiya: 'Yan Kasar Jamus Basa Zaben Shugaban Kasa Kai tsaye, duba nasu tsarin zaben

Duk da cewar kasar Jamus na bin tsarin dimokradiyya ne amma 'yan kasar basu keda ikon zaben shugaban kasa ba kamar yadda yake a Najeriya da sauran kasashe masu bin tsarin dimokradiyya.

Kimanin 'yan kasar Jamus mutum miliyan 61.5 'yan sama da shekara 18 ne suka kada kuri'a a zaben na jiya, wato 24 ga watan satumba, domin zaben 'yan majalisu.

Zaben Kasar Jamus da aka kammala jiya: 'Yan Kasar Jamus Basa Zaben Shugaban Kasa Kai tsaye, duba nasu tsarin zaben
Angela Merkel

A yayin kada kuri'a a kasar ta Jamus ana bawa mai zabe kuri'u guda biyu ne; daya ta zaben dan majalisa da ake kira "German Bundestag", daya kuma ta zaben jam'iyya. Mutumin da ya fi samun kuri'u mafi rinjaye shine zai wakilci mutanen mazabarsa a majalisar kasa sannan jam'iyyar data samu kuri'u mafiya rinjaye ta fitar da Shugaban kasa da a kasar ta Jamus ake kira "Chancellor". Jam'iyyu kanyi hadaka ko maja domin samun rinjayen fitar da "Chancellor"

DUBA WANNAN: Kimiyya: Shin ina ne asalin dan-Adam, kuma meye alakarsa da sauran halittun duniya?

Uwargida Angela Merkel ce ta kara samun nasarar haye kujerar ta "Chancellor" a Karo na hudu kuma a karo na farko a tarihin kasar ta Jamus.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng