Wasu Jiragen Yaki Sun Yi Taho Mu Gama a Sararin Sama, Sun Tarwatse a US

Wasu Jiragen Yaki Sun Yi Taho Mu Gama a Sararin Sama, Sun Tarwatse a US

  • Rahotanni sun bayyana cewa wasu Jiragen yaƙi biyu sun karo da juna a sararin sama kana suka fashe a garin Dellas na ƙasar Amurka
  • Ance jiragen na shawagin tuna wa da yaƙin duniya na II lokacin da lamarin ya faru, zuwa yanzun an tabbatar da mutuwar 2
  • Hukumomi sun ce za'a rufe Filin jirgin har zuwa lokacin da jami'ai suka kammala bincike kan abinda ya haddasa haɗarin

Aƙalla mutum biyu ne aka rahoto sun mutu yayin da Jiragen yaƙi biyu da suka halarci yaƙin duniya na II suka yi karo da juna a ranar Asabar a Dallas, ƙasar Amurka.

Wani bidiyo da ke yawo a Intanet ya nuna yadda jiragen biyu dake shawagi a sama suka ci karo da juna, kana suka tarwatse tun a sama suka kama da wuta.

Kara karanta wannan

Karin Bayani: Wani 'Bam' Ya Tashi a Babban Birnin Wata Jihar Arewa

Karon jiragen sama biyu.
Wasu Jiragen Yaki Sun Yi Taho Mu Gama a Sararin Sama, Sun Tarwatse a US Hoto: channelstv
Asali: UGC

Jiragen biyu a cewar rahoton Premium Times, suna bikin shawagin tuna wa da yaƙin ne a filin sauka da tashin jirage na Dallas Executive Airport.

Har yanzun da muke kawo muku wannan rahoton babu cikakken bayani kan adadin mutanen da wannan mummunan hatsarin na karo ya rutsa da su.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Amma a rahoton BBC, Ƙungiyar matuƙan jiragen sama data wakilci hukumar matuƙan jirgin sama ta ƙasar Amurka, tace Terry Barker da Len Root, wasu tsofaffin mambobinta na cikin waɗanda suka mutu a haɗarin.

Haka zalika an baygana sunayen jiragen da, Boeing B-17 Flying Fortress da kuma smaller Bell P-63 Kingcobra.

"Har yanzun ba'a tabbatar da adadin mutanen da lamarin ya shafa ba amma babu wanda karon ya shafa daga cikin mutanen dake wurin tsaye," inji Eric Johnson, magajin garin Dellas.

Kara karanta wannan

Tashin Hankali: Wasu Ɗalibai Biyu Na Wata Jami'a a Najeriya Sun Mutu a Ɗakin Kwana

Ya kuma ƙara da cewa ma'aikatar Sufurin jiragen sama ta ƙasar ce ke jagorantar bincike kan abinda ya hadda karon jiragen kuma Filin jirgin zai ci gaba da zama a rufe har sai an kammala bincike.

Wani Jirgin Sama Ɗauke Da Mutane Ya Yi Hatsari a Tanzaniya

A wani labarin makamancin wannan kun ji cewa Wani Jirgin Sama Ɗauke Da Mutane Ya Yi Hatsari, Ya Afka Cikin Kogin Victoria

An tattaro cewa jirgin ya shiga matsala ne biyo bayan haɗuwar hadari tare da fara saukar ruwa yayin da ya zi sauka a filin jirgin Bukoba.

Shugabar Tanzaniya, Samia Suluhu Hassan, ta yi kira al'umma sun fawwala wa Allah komai yayin da jami'ai suka dira wurin domin fara aikin ceto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel