Gwamnati Ta Fusata, Ta Dakatar da Musulmai kan ‘Shirin’ Kafa Tsarin Musulunci a Jamus

Gwamnati Ta Fusata, Ta Dakatar da Musulmai kan ‘Shirin’ Kafa Tsarin Musulunci a Jamus

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Berlin, Germany - Ma’aikatar cikin gida a kasar Jamus ta sanar da daukar mataki kan wata kungiyar Musulmai da ta fara yaduwa a kasar.

Jamus ta haramta ƙungiyar Muslim Interaktiv, wadda ake zargi da shirin aiwatar da abubuwan da suka saba kundin tsarin mulki.

Jamus ta hana wasu Musulmai shirin kafa tsarin Musulunci
Minisan cikin gida a Jamus, Alexander Dobrindt, Muslim Interaktiv. Hoto: TOBIAS SCHWARZ/AFP, Gregor Fischer.
Source: Getty Images

Jamus ta takawa kungiyar Muslim Interaktiv birki

Rahoton ABC News ya tabbatar da cewa daga cikin zarge-zargen da ake yi wa kungiyar har da kira na kafa tsarin Musulunci.

Kara karanta wannan

Kungiyar Yarbawa ta fallasa shirin Trump kan Shugaba Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jami’an tsaro sun gudanar da samame a akalla gidaje bakwai a birnin Hamburg, inda ƙungiyar ta yi sansani tun 2020.

Ministan cikin gida, Alexander Dobrindt daga jam'iyyar CDU/CSU, ya ce gwamnati ba za ta amince wasu su rusa tsarin dimokuraɗiyyar Jamus da kalaman kiyayya ba.

Ya tabbatar da cewa:

“Ba za mu bari ƙungiyoyi irin Muslim Interaktiv su lalata ƙasarmu daga cikin gida ba.”
Jamus ta takawa kungiyar Muslim Interaktiv birki
Yan kungiyar Muslim Interaktiv suna zanga-zanga a Hamburg, Jamus. Hoto: Gregor Fischer.
Source: Getty Images

Zargin Muslim Interaktiv kan gwamnatin Jamus

Ƙungiyar ta jawo hankalin jama’a tun watan Afrilu 2024 lokacin da ta shirya zanga-zanga da mutane sama da 1,200 a Hamburg, inda masu zanga-zangar suka zargi gwamnatin Jamus da wariyar addini ga Musulmi.

Wasu daga cikin masu zanga-zangar sun rike rubuce-rubuce kamar “tsarin Musulunci shi ne mafita”, lamarin da ya jawo ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar, cewar The Washington Post.

Ministan cikin gida a kasar ya ce an riga an dakatar da ƙungiya da ake zargin tana take hakkin mata da kuma nuna kiyayya ga Isra'ila, za kuma a kwace kadarorin kungiyar.

Kara karanta wannan

Magana ta girma: EU ta tsoma baki game da barazanar Amurka kan Najeriya

Jami'an tsaro sun ce ƙungiyar na amfani da kafafen sada zumunta wajen yada ra'ayin cewa gwamnati da al’umma suna ware Musulmi.

Ministan cikin gida na Hamburg, Andy Grote, ya ce wannan mataki ya kawar da hatsarin ƙungiya mai tsattsauran ra’ayi wanda ake ganin barazana ce.

Haka kuma, ’yan sanda sun yi bincike a Berlin da jihar Hesse game da wasu ƙungiyoyi biyu da suka hada da 'Generation Islam' da 'Realitaet Islam'.

Tun baya, Jamus ta taba haramta wasu ƙungiyoyin Musulmi, ciki har da Ansaar a 2021, bisa zargin taimakon ƙungiyoyin ta’addanci da sunan agaji.

'Dan siyasa a Jamus ya karbi Musulunci

A baya, an ji cewa addinin Musulunci na kara samun karbuwa a kasar Jamus bayan wani rikakken mai adawa da addinin Musulunci ya Musulunta.

Wagner yana cikin masu sukar Musulmai a kasar ta Jamus inda aka ce dan siyasar ya karbi addinin Musulunci.

An ce jam'iyyar AfD na da ra’ayin rikau wajen takurawa Musulmai, sai ga shi wanda ke cikin manyan ta a kasar ya shiga Musulunci.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.