Daga karshe, an amince a kira Sallah da Lasfika sau daya a mako a kasar Jamus

Daga karshe, an amince a kira Sallah da Lasfika sau daya a mako a kasar Jamus

  • Bayan shekara da shekaru, Musulmai zasu fara kiran Salla ranar Juma'a
  • An baiwa Masallatai mintuna 5 kacal Ladan ya kira Sallah
  • Kimanin Musulmai milyan hudu da rabi ke zama a kasar Jamus.

Hukumomi a birnin Cologne dake kasar Jamus sun rattafa hannu kan yarjejeniya da al'ummar Musulmi don amfani da lasfika wajen kiran Sallah ranar Juma'a, gwamnati ta sanar.

Daga yanzu, an baiwa dukkan Masallatai 35 dake Cologne mintuna biyar ranar Juma'a tsakanin karfe 12 da 3 domin su kira Sallah da na'urar amsa kuwa, rahoton Reuters

Wannan sabuwar yarjejeniya na shekaru biyu ne kacal.

Wannan ya hada da Babban Masallacin Cologne wanda ginashi a 2018 ya tayar da tarzoma a kasar Jamus.

Shugabar birnin Cologne, Mayor Henriette Reker, ta bayyana cewa barin Musulmai su rika kiran Sallah alamun girmama juna ne.

Kara karanta wannan

Jerin matasan Najeriya 6 da suka hau kujerun gwamnoni, sun dauki tsauraran matakai

A gajeren maganar da ta saki a shafin na Tuwita, tace:

"Bari Ladan ya kira Sallah a fahimtana abune mai kyau na girmama juna. Yana nuna cewa ana baiwa kowa yancin addidninsa a Cologne."

Daga karshe, an amince a kira Sallah sau daya a mako a kasar Jamus
Daga karshe, an amince a kira Sallah sau daya a mako a kasar Jamus Hoto: Wolfgang Rattay/Reuters
Asali: UGC

An kwatanta kiran Sallan ne da kararrawan da cocin Cologne ke bugawa.

Gwamnatin Cologne tace za'ayi kiran Sallan ne kadai ranar Juma'a kuma bisa ka'idojin karar lasfika kuma a sanar da makwabta kafin a yi.

Kimanin Musulmai milyan hudu da rabi ke zama a kasar Jamus.

Jamus, Kasashen Turai sun ba Najeriya gudumuwar Naira Biliyan 20 domin gyara wuta

Leadership tace kungiyar EU ta kasashen nahiyar Turai ta amince ta kara bada fam miliyan €15 ga Najeriya domin tallafa wa shirin wutan NESP.

Hakan na zuwa ne a lokacin da aka bada sanarwar kulla yarjejeniyar EU da kungiyar Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit, watau GIZ.

Kara karanta wannan

Jerin Fitattun Jaruman Kannywood 5 da suka taba fitowa takarar siyasa da kujerun da suka nema

Kungiyar kasar Jamus za ta bada fam miliyan €48 domin bunkasa shirin NESP a shekara mai zuwa.

Matakin da Deutsche Gesellschaft für Internationale Zusammenarbeit ya dauka ya sa kungiyar EU ta kara gudumuwarta a kan miliyan €20 da ta bada a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel