Addinin Musulunci na kara samun karbuwa a kasar Jamus
- Wani rikakken mai adawa da addinin Musulunci yayi ridda
- Wagner yana cikin masu sukar Musulmai a kasar Jamus
- Yanzu haka dai ‘Dan siyasar ya karbi addinin Musulunci
Wani babban ‘Dan adawan addinin Musulunci a kasar Jamus ya bar addinin sa inda ya karbi musulunci har ta sa yayi murabus daga matsayin sa a Jam’iyyar su. Yanzu haka babu suna mai tashe a Kasar irin Muhammadu.
Jaridun kasar waje sun bayyana cewa Arthur Wagner wanda yana cikin Jam’iyyar da ke adawa da addinin Musulunci a kasar Jamus yayi ridda daga Kiristanci ya kuma koma Musulmi yanzu. Hakan ta sa ya bar Jam’iyyar AfD.
KU KARANTA: An nemi Shugaba Buhari ya kawo karshen Almajiranta
Kowa dai ya san Jam’iyyar AfD da ra’ayin rikau wajen takurawa Musulmai, sai ga shi wanda yana cikin manyan ta a kasar ya shiga Musulunci. Yanzu haka dai Jam’iyyar ta AfD tana cikin manyan Jam’iyyun kasar ta Jamus.
A baya Wagner yana cikin wadanda su kayi adawa da Shugabar kasar Jamus Angela Merkel saboda ba da damar Musulmai su shigo cikin kasar. Sai dai ga shi kwatsam aka ji wannan Dattijo ya karbi addinin Islama dare daya.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng