Babu ruwan Musulunci da ta'addanci - shugabar kasar Jamus Angela Merkel

Babu ruwan Musulunci da ta'addanci - shugabar kasar Jamus Angela Merkel

-Shugabar Jamus ta kare musulunci a wani babban taro na kasa da kasa da aka yi a birinin Munich a inda da ta gabatar da jawabi

-Angela Merkel ta tsame addinin musulunci daga ayyukan ta'addanci tare da yin kira ga malaman addinin da su hada hannu su yaki bata sunan da ake yiwa addinin

Babu ruwan Musulunci da ta'addanci - shugabar kasar Jamus Angela Merkel
Babu ruwan Musulunci da ta'addanci - shugabar kasar Jamus Angela Merkel

Shugabar kasar Jamus Angela Merkel ta ce babu abin da ya hada addinin Musulunci da ta'addanci.

Shugabar ta fadi haka ne a wani jawabi da ta yi a wani taro da aka na kasa da kasa kan tsaro a birnin Munich na kasar Jamus a ranar Asabar 18 ga watan Fabarairu na shekarar 2017.

A cewar gidan talbijin na Al Jazeera, shugaba Merkel ta kuma yi kira ga malaman addinin musulunci da su hada hannu, su kuma tashi tsaye su yaki wannan bata sunan da ake yiwa addinin ta hanyar shafa masa kashin kaji, wanda 'yan ta'addan ke yi ta hanyar fakewa da shi suna aikata barna.

Angela ta kuma shaidawa taron cewa, wannan mataki na malaman shi ne kadai zai nunawa wadanda ba musulmai ba cewa lallai addinin muslunci addinin zaman lafiya ne. An kumayi masa mummunan fahimta ne

Merkel wacce ta dade ta na sukar manufofin shugaban Amurka Donald Trump na hana 'yan wasu wasu kasashe musulmai 7 shiga Amurka, ta kuma ce,

"Ina fatan manyan masu fada a ji za su fito da wata hanyar da za su yi amfani da ita, na wajen rarrabewa duniya tsakanin koyarwar muslunci na hakika, da kuma masu aikata ta'addanci da sunan musuluncin".

"Mu da ba musulmai ba, ba za mu iya yin haka ba, dole ne sai dai shaihunnan malamai da kuma hukumomin musulunci".

A watan satumbar shekarar 2015 ne kasar Jamus ta ya kyale dubban 'yan gudun hijirar Siriya wacce kasar larabawa ce kuma musulma suka kwarara zuwa cikin kasar Jamus saboda tausayawa da kuma taimako, kamar yadda ta yi bayani a taron

Babban taron na kasa da kasa kan tsaro ya samu halartar shugabannin kasashe, ciki har da mataimakin shugaban kasar Rasha da kuma Mista Mike Pence na Amurka.

Ga ra'ayin jama'a kan rashin lafiyar shugaba Buhari

Asali: Legit.ng

Online view pixel