An Samu Barkewar Cutar Ebola, Mutane 15 Sun Mutu yayin da Aka Killace 28 a DR Congo

An Samu Barkewar Cutar Ebola, Mutane 15 Sun Mutu yayin da Aka Killace 28 a DR Congo

  • Hukumomin lafiya sun tabbatar da mutuwar mutane 15, ciki har da ma’aikatan lafiya huɗu, yayin da cutar Ebola ta barke a kasar Congo
  • Akalla mutum 28 ne ake zargin suna dauke da cutar a lardin Kasai, inda aka gano wata kwayar Ebola da ake kira da Zairense
  • Hukumar lafiya ta duniya ta ce yanzu haka tana aiki cikin gaggawa domin dakile yaduwar cutar tare bayyana matakan da ta fara dauka

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kinshasa - Ma'aikatar lafiya ta Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DR Congo), ta ce akalla mutane 15 sun mutu a yayin da aka samu bullar sabuwar cutar Ebola a kasar.

Ma'aikatar ta bayyana cewa, an fara tabbatar da bullar cutar ne a jikin wata mata mai shekaru 34 da ke da dauke juna biyu.

Kara karanta wannan

'Laifi ne': Za a hukunta yan mata da ke saba alkawari bayan karbar kudin samari

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ma'aikatan lafiya 4 ne cikin mutane 15 da suka mutu saboda kamuwa da Ebola a Congo
Ma'aikatan lafiya na gudanar da gwaji ga wata da ake zargin ta kamu da Ebola a Dr. Congo. Hoto: SDI Productions
Source: Getty Images

Cutar Ebola ta sake barkewa a DR Congo

An ce an ga alamomin cutar a jikin matar, wacce aka kwantar da ita a asibiti a watan da ya gabata, wadanda suka haɗa da zazzaɓi mai zafi da amai, inji rahoton BBC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan shi ne karo na 16 da cutar Ebola ke barkewa a wannan kasa da ke a tsakiyar Afirka, wadda ke da raunin tsarin kiwon lafiya.

Sabuwar cutar ta barke ne a lardin Kasai da ke tsakiyar kasar Congo, inda aka kwantar da akalla mutane 28 da ake zargin sun kamu da cutar, inji ma'aikatar.

Ebola: Mutane 15 sun mutu a kasar Congo

A wani ɓangare na yaƙar cutar Ebola, Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta ce ta fara “aiki cikin azama don dakatar da yaɗuwar cutar da kuma kare jama'ar Congo."

Hukumar ta ce ma'aikatan lafiya huɗu na daga cikin mutane 15 da suka mutu bayan barkewar cutar a lardin Kasai.

Kara karanta wannan

Burkina Faso ta tsaurara doka, gwamnatin Soja ta dauki mataki a kan auren jinsi

Kafar labarai ta Aljazeera ta rahoto WHO ta ƙara da cewa:

"Adadin masu kamuwa da cutar na iya ƙaruwa yayin da cutar ke ci gaba da yaɗuwa. Yanzu aiki na hannun tawagar da ke ba da agajin gaggawa da kuma tawagogin kasar.
"Hadin gwiwar tawagogin za su yi aiki don gano mutanen da ke cikin hadarin kamuwa da cutar, kuma suke buƙatar kulawar gaggawa, don tabbatar da cewa an killace su."
An ce cutar Ebola ta fara bulla ne a shekarar 1976 a kogin Ebola da yanzu ake kira DR Congo.
Ma'aikaciyar lafiya tana yi wa wata mata allurar rigakafin Ebola a Uganda. Hoto: BADRU KATUMBA / Contributor
Source: Getty Images

Yadda Ebola ta samo asali a DR Congo

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce DR Congo tana da "tarin magunguna," ciki har da allurai 2,000 na rigakafin Ervebo, "wadda ke da tasiri wajen kare mutane daga wannan nau'in cutar."

An fara gano kwayar cutar, wadda ake tunanin ta samo asali ne daga jemagu masu cin 'ya 'yan itace, a shekarar 1976 kusa da kogin Ebola a yankin da yanzu ake kira DR Congo.

Mutane na kamuwa da cutar ne lokacin da suka yi mu'amala ta kai tsaye da, fatar jiki, jini, amai, bayan gida ko ruwan jikin wani da ke dauke da cutar Ebola.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun cinnawa gidaje 30 wuta a Filato, mutum 300 sun shiga garari

An samu bullar cuta mai kama da Ebola

A wani labarin, mun ruwaito cewa, a lokacin da kasar Guinea ke murnar kawar da cutar Ebola, an samu bullar sabuwar annoba da aka yi wa lakabi da Marbug.

Gueckedou, inda aka tabbatar da bullar cutar Marburg, shi ne yankin da aka samu bullar cutar Ebola a 2021 da kuma shekarar 2014 zuwa 2016.

A cewar WHO, cutar ta samo asali ne daga cikin jemagu kuma tana iya bazuwa tsakanin mutum zuwa mutum ta zufar jiki ko idan yawun mutum ya zuba kan abubuwa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com